Bayan Rasa Saurata kan Kushe Gwamnatin PDP, An Bukaci Sanata Ya Nemi Gwamna
- Bayan rasa sarautarsa a jihar Bauchi, an bukaci Sanata Shehu Buba ya nemi takarar gwamnan a zaben 2027
- Kungiyar Shehu Buba Umar Vanguard (SBUV) ta bayyana irin gudunmawa da Sanatan ya bayar a siyasar Bauchi
- Wannan na zuwa ne bayan masarautar Bauchi ta tube sa daga sarautar Mujaddadi saboda sukar Bala Mohammed
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Bauchi - Ƙungiya ta bukaci Sanata Shehu Buba ya nemi takarar gwamnan jihar Bauchi a zaben 2027.
Kungiyar Shehu Buba Umar Vanguard (SBUV) a Bauchi ita ta bukaci hakan duba da gudunmawarsa a siyasa.
An bukaci Sanata Buba ya nemi gwamnan Bauchi
Shugaban kungiyar, Injiniya Ishaq Dabo ya bayyana haka a yau Juma'a 6 ga watan Satumbar 2024, cewar rahoton Tribune.
Ishaq ya ce yanzu ne Sanatan Bauchi ta Kudu ya kamata ya fara shiri saboda da safe ake kama fara.
Wannan kira na zuwa ne makwanni kadan bayan tube Sanatan daga sarauta a Bauchi kan sukar Gwamna Bala Mohammed.
Masarautar ta tube Sanatan daga sarautar Mujaddadin Bauchi saboda rashin dattaku daga Shehu Buba game da gwamnan jihar.
An bayyana gudunmawar Sanata Shehu Buba
"Dan siyasa daya ne a jihar Bauchi wanda zai iya kwace mulki daga PDP duba da kwarewar da ya ke da ita a siyasance."
"Mu na da tabbacin cewa Shehu Buba zai cirewa Bauchi kitse a wuta da cigaba fiye da yadda take a yanzu."
- Ishaq Dabo
Kungiyar ta ce duk da sanatan yana wakiltar Bauchi ta Kudu amma har sauran yankuna bai bari ba wurin ba da gudunmawarsa a jihar.
Sanatan Bauchi ya magantu bayan rasa sarauta
Kun ji cewa Sanatan Bauchi ta Kudu, Shehu Buba ya yi martani kan tube shi da aka yi daga sarautar Mujaddadi bayan sukar gwamnan Bauchi.
Sanata Buba ya ce ya karbi wannan hukunci hannu biyu-biyu inda ya roki Allah ya kawo mai ceton jihar daga wannan kangi
Hakan na zuwa ne bayan tsige shi daga sarauta da masarautar Bauchi ta yi kan sukar Gwamna Bala Mohammed kwanan nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng