Daga Karshe, INEC Ta Fadi Dalilin Sanar da Nasarar Tinubu da Tsakar Dare a 2023
- Hukumar zabe ta fayyace dalilin sanar da sakamakon zaben shugaban kasa da tsakar dare wanda Bola Tinubu ya yi nasara
- INEC ta ce hakan bai rasa nasaba da tattara sakamakon zaben 2023 wanda ya kunshi jihohi da dama da dole sai an jira su
- Martanin na zuwa ne yayin da a wancan lokaci ake ta korafi kan sanar da sakamakon zaben da misalin karfe 2:00 na dare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Hukumar zabe ta INEC ta yi magana kan ce-ce-ku-ce da ake yi game da sanar da babban zaben 2023.
Hukumar ta ce dole ce ta saka INEC sanar da sakamakon zaben da tsakar dare wanda Bola Tinubu ya samu nasara.
INEC ta yi magana kan nasarar Tinubu
Sakataren yada labaran hukumar, Rotimi Oyekanmi shi ya bayyana haka a yau Juma'a 6 ga watan Satumbar 2024, cewar The Guardian.
Oyekanmi ya ce dole shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ya jira dukan sakamakon zaben daga sauran jihohi kafin sanarwa.
Ya ce hakan ya zama dole duba da yadda ake tattara sakamakon zaben daga matakin mazabu da zuwa unguwa da kananan hukumomi da jihohi da kuma matakin kasa, kamar yadda Tribune ta ruwaito.
Har ila yau, Oyekanmi ya ce Farfesa Yakubu ya jira sakamakon daga jihohi masu nisa kamar Sokoto da Borno zuwa Abuja kamar yadda doka ta tanadar.
Musabbabin sanar da sakamakon zabe da dare
"A zaben shugaban kasa, ana daukarta kamar mazaba daya ce, dole za a fara tattara sakamako daga mazabu zuwa unguwanni da kananan hukumomi kafin zuwa matakin kasa tare da sanarwa a Abuja."
"Amma mutane sun yi ta korafi bayan sanar da sakamakon zabe da karfe 2:00 na dare saboda ba su fahimci yadda abin ya ke ba."
"Dole shugaban hukumar ya jira sakamakon zaben jihohi 36 ciki har da sauran jihohi da suke da nisa kamar Borno da Sokoto."
- Rotimi Oyekanmi
INEC ta magantu kan sahihancin zaben Tinubu
Kun ji cewa hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta bayyana cewa babu wani tuntuɓen alkalami ko ruɗani a sakamakon zaben shugaban ƙasa na 2023.
Hukumar INEC ta jaddada cewa sakamakon zaɓen da aka ji daga bakinta bayan kammala kaɗa kuri'u a 2023 sahihi ne kuma ingantacce.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng