“Tarwatsewa Za Ta Yi”: Minista Ya Fadi Abin da Zai Faru Idan Ya bar Jam’iyyarsa
- Tsohon gwamnan Rivers, Nyesom Wike ya yi barazana ga jam'iyyar PDP idan har suka fusata shi ya fice daga cikinta
- Wike ya ce da zarar ya fusata har ya gudu daga PDP to tabbas karshenta ya zo kuma dubban yan jam'iyyar za su fita
- Ministan harkokin birnin Abuja ya bayyana haka ne a sakatariyar jam'iyyar da ke birnin Port Harcourt a jihar Rivers
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Ministan Abuja, Nyesom Wike ya fadi abin da zai faru da PDP idan ya fice daga cikinta.
Nyesom Wike ya ce da zarar ya fice daga jam'iyyar tarwatsewa za ta yi tare da cin karo da tarun matsaloli.
Wike ya yi barazana ga jam'iyyar PDP
Tsohon gwamnan Rivers, Nyesom Wike ya bayyana haka a sakatariyar jam'iyyar a Port Harcourt da ke jihar Rivers, cewar rahoton Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Barazanar Wike na zuwa ne bayan gwamnonin PDP sun nuna goyon bayansu ga Gwamna Siminalayi Fubara da ke fada da Wike.
Gwamnonin sun bayyana haka ne birnin Jalingo da ke jihar Taraba a ranar 23 ga watan Agustan 2024.
Sai dai Wike ya yi musu barazana inda ya ce yana fita PDP za ta tarwatse kuma ba za ta sake dawowa hayyacinta ba.
Wike ya ce jam'iyyar PDP za ta watse
"Idan yau dinnan na ce zan fita a PDP zuwa wata jam'iyya za ta samu matsala, amma za mu zauna inda muke."
- Nyesom Wike
Wike ya kara da cewa da zarar ya fice daga PDP, dubban yan jam'iyyar da dama za su fice domin binsa inda ya ke.
An bukaci a kama Wike da gaggawa
Kun ji cewa jagoran yan kabilar Ijaw a Najeriya, Edwin Clark ya umarci shugaban yan sandan Najeriya da ya gaggauta cafke ministan Abuja.
Edwin Clark ya ce ministan Abuja ya cancanci a kama shi saboda kalaman tayar da hankali da ya yi a wajen taro.
Wike ya ce zai tayar da hankali ne a jihohin PDP yayin wani taron jam'iyyar a birnin Fatakwal a ranar Lahadi da ta gabata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng