Shugaban Karamar Hukumar da Aka Tsige Ya Fice daga APC, Ya Tsaya Takara a PDP

Shugaban Karamar Hukumar da Aka Tsige Ya Fice daga APC, Ya Tsaya Takara a PDP

  • PDP ta ba tsohon shugaban ƙaramar hukumar Ijebu ta Gabas, Chief Wale Adedayo damar tsayawa takara bayan tantance shi
  • Kansiloli sun tsige Adedayo daga kujerar ciyaman ne bayan ya zargi Gwamna Ogun da laifin satar kuɗin kananan hukumomi
  • Sai dai bayan haka ya fice daga APC zuwa PDP domin sake neman kujerar shugaban ƙaramar hukumar Ijebu ta Gabas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ogun - Tsohon shugaban ƙaramar hukumar Ijebu ta Gabas a jihar Ogun, Wale Adedayo ya sake tsayawa takarar ciyaman a karkashin inuwar PDP.

Jam'iyyar PDP reshen jihar Ogun ta tantance Adedayo sannan ta amince ya shiga a fafata da shi a zaɓen fitar da ɗan takara wanda za a yi ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Nenadi Usman: An naɗa mace a matsayin shugabar jam'iyya ta ƙasa a Najeriya

Chief Wale Adedayo.
Ogun: Tsohon shugaban ƙaramar hukumar da aka tsige ya bar APC, ya tsaya takara a PDP Hoto: Chief Wale Adedayo
Asali: Twitter

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da sakataren watsa labaran PDP na jihar Ogun, Afolabi Orekoya, ya rabawa manema labarai ranar Laraba, Daily Trust ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa aka tsige shugaban ƙaramar hukumar?

Idan ba ku manta ba an tsige Adedayo daga kujerar ciyaman na ƙaramar hukumar Ijebu ta Gabas saboda ya zargi gwamna Dapo Abiodun da satar kuɗin kananan hukumomi.

Sai dai bayan sauke shi, Mista Adedayo ya fice daga jam'iyyar APC zuwa PDP domin sake tsayawa takarar shugaban ƙaramar hukumar.

Mai magana da yawun PDP ya ce jam'iyyar ta tantance shi kuma ta ba shi damar neman tikitin takara a zaben fitar da ɗan takara da za a yi a ƙarshen mako, in ji Punch.

Ogun: PDP ta tantance Adedayo

"Daruruwan ‘yan takara daga mazabu 236 da kananan hukumomi 20 a Ogun ne suka sayi fom ɗin tsayawa takara kuma an tantance su.

Kara karanta wannan

Gwamna ya shiga tsaka mai wuya, jam'iyya ta fara shirin ɗaukar mataki a kansa

"Daga cikin ‘yan takarar da aka tantance a sakatariyar PDP da ke Abeokuta, akwai tsohon shugaban ƙaramar hukumar Ijebu ta Gabas, Cif Wale Adedayo wanda ke neman komawa kan kujerarsa ta ciyaman.
"PDP ta tsayar da ranakun Alhamis, 5, da Asabar 7 ga watan Satumba a matsayin ranakun da za a gudanar da zabukan fitar da gwani na kansiloli da na ciyamomi a mazabun 236 da kananan hukumomi 20."

- Afolabi Orekoya.

Gwamnan Ogun ya tallafawa ɗalibai

A wani rahoton kuma gwamnatin jihar Ogun ta fara rabon kudi N10,000 ga daliban firamare da sakandare saboda halin kunci da ake ciki.

Gwamna Dapo Abiodun ya ce akalla dalibai 100,000 za su ci wannan gajiya ta kyautar kudin a makarantun gwamnati guda 2,000 a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262