Ganduje da APC Sun Samu Koma Baya Ana Saura 'Yan Kwanaki Zaben Gwamnan Edo
- Jam'iyyar APC mai adawa a Edo ta samu koma baya yayin da ake tunkarar zaɓen gwamnan jihar da za a yi a a Satumba
- Wani tsohon ɗan majalisar dokokin jihar Edo kuma jigo a APC ya sanar da yin murabus daga zama 'dan jam'iyyar
- Honarabul Emmanuel Agbaje ya yanke shawarar ficewa daga APC ne saboda an mayar da shi saniyar ware a jam'iyyar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Edo - Jam'iyyar APC ta samu koma baya a jihar Edo ana saura kwanaki kaɗan a gudanar da zaɓen gwamnan jihar.
Jigo a jam'iyyar kuma tsohon ɗan majalisar dokokin jihar wanda ya wakilci Akoko-Edo II daga 2015 zuwa 2023, Honarabul Emmanuel Agbaje ya yi murabus daga zama mamba a APC.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa ya sanar da ficewarsa daga APC ne a cikin wata wasiƙa da ya aikawa shugaban jam'iyyar na mazaɓa ta 10 a ƙaramar hukumar Akoko-Edo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa jigon ya fice daga APC?
A cikin wasiƙar mai ɗauke da kwanan watan 2 ga watan Satumba 2024, Agbaje ya koka kan yadda aka mayar da shi saniyar ware wajen gudanar da harkokin jam'iyyar a mazaɓarsa.
"Ban ɗauki wannan matakin haka nan kawai ba, sai bayan da na tattauna da magoya baya na da shugabanni. Na yi amanna cewa hakan shi ne abin da yafi dacewa na yi a wannan lokacin."
"Tun da dimokuraɗiyya ta ba mu damar zaɓar abin da muke so, ina da ƴancin neman wurin da suke mutunta biyayya da sadaukarwa."
"Ba zan iya ci gaba da amincewa a mayar da ni da sauran ƴan jam'iyya na asali saniyar ware ba a mazaɓa ta."
- Honorabul Emmanuel Agbaje
Ɓaraka ta kunno kai a jam'iyyar APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsagin APC reshen Arewa ta Tsakiya ya zargi masu goyon bayan Abdullahi Umar Ganduje ya ci gaba da zama shugaban jam'iyyar da son zuciya.
Kungiyar APC ta Tsakiya karkashin jagorancin shugabanta, Saleh Zazzaga ta zargi tsohon shugaban majalisa, Ameh Ebute da son rai bisa kalamansa kan Ganduje.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng