“Mu Na Son Sauyi”: An ba Atiku, Tinubu da Peter Obi Shawara kan Sake Takara a 2027

“Mu Na Son Sauyi”: An ba Atiku, Tinubu da Peter Obi Shawara kan Sake Takara a 2027

  • An ba Shugaba Bola Tinubu da Atiku Abubakar da Peter Obi shawara kan sake tsayawa takara a zaben 2027 domin sababbin fuskoki
  • Tsohon kakakin kamfen jam'iyyar LP, Kenneth Okonkwo ya ce ya kamata dukansu su janye sake tsayawa takara a zaben
  • Okonkwo ya ce jam'iyya mai mulki ta gaza tabuka wani abu da kuma cika alkawuran da ta daukawa 'yan kasa lokacin kamfe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon kakakin kamfe na jam'iyyar LP, Kenneth Okonkwo ya shawarci 'yan takarar shugaban kasa kan zaben 2027.

Kenneth Okonkwo ya shawarci Peter Obi da Bola Tinubu da Atiku Abubakar su kauracewa neman takara a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

'Tinubu ya shaƙe wuyan talaka,' Dan takarar shugaban kasa ya dura kan gwamnati

An shawarci Atiku da Obi da kuma Atiku su hakura da takara a zaben 2027
An ba Atiku, Tinubu da Peter Obi shawara da su hakura da neman takara a zaben 2027. Hoto: Atiku Abubakar, Asiwaju Bola Tinubu, Peter Obi.
Asali: Facebook

An shawarci Atiku, Tinubu kan takarar 2027

Okonkwo ya bayyana haka ne yayin hira a gidan talabijin na Arise a yau Laraba 4 ga watan Satumbar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon jigon jam'iyyar LP ya ce a yanzu ana bukatar sababbin fuska a zaben 2027 saboda samun sauyi a kasa.

Yayin hirar da Punch ta leko, Okonkwo ya ce dalilin shi ne sun gaza cika alkawuran da suke dauka da kuma rashin hadin kan 'yan adawa.

Ya kuma caccaki 'yan adawa kan rashin hada kai wanda ya yi sanadin rashin samun kujerun shugaban Majalisar Wakilai da mataimakinsa.

Ana bukatar sababbin fuskoki a zaben 2027

"Na yarda dari bisa dari ya kamata mu samu sababbin fuska wanda shi ne dalilina na cewa Atiku da Tinubu da Obi ya kamata su kauce."
"Saboda jam'iyya mai mulki ta gaza kuma 'yan adawa sun gagara hada kai domin samun wasu matsayi kowa ya sani yan adawa sun fi yawa a Majalisar Wakilai.'

Kara karanta wannan

"Za mu bi maku hakkin ku," Tinubu ya sha alwashi kan kisan Bayin Allah a Yobe

"Bai kamata ana kammala zabe kuma abin da za aka fara shiri a kai shi ne zaben gaba ba, ya kamata a hada wata tafiya mai karfi a matsayin yan adawa."

- Kenneth Okonkwo

Okonkwo ya ce idan har yan adawa a Majalisar Wakilai sun hada kai da sun samu mukamin shugaban Majalisar da kuma mataimakinsa.

Kwankwaso ya soki shirin hadakar yan adawa

Kun ji cewa jigon jam'iyyar APC a jihar Kano ya yi magana kan shirin hadakar Atiku Abubakar da Peter Obi da Rabiu Kwankwaso.

Musa Ilyasu Kwankwaso ya ce duka bata lokacinsu suke yi wurin hadaka saboda zaben 2027 domin kuwa hadama ta yi masu yawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.