‘Tinubu Ya Shaƙe Wuyan Talaka,’ Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Dura kan Gwamnati

‘Tinubu Ya Shaƙe Wuyan Talaka,’ Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Dura kan Gwamnati

  • Dan takarar shugaban kasa a a zaben 2023 kuma jagoran jam'iyyar SDP, ya yi zazzafan martani ga gwamnatin tarayya
  • Adewole Ebenezer Adebayo ya ce gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta shake wuyan talakawan Najeriya gam
  • Haka zalika Adewole ya ce gwamnati a karkashin Tinubu ta gaza cika alkawarin da ta dauka a kundin tsarin mulkin kasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya na cigaba da shan suka da tsare tsaren da masana ke gani sun jefa al'umma a wahalar rayuwa.

Dan takarar shugaban kasa a SDP, Adewole Ebenezer Adebayo ya ce shugaba Bola Tinubu ya tsanantawa talakawan Najeriya.

Kara karanta wannan

"Za mu bi maku hakkin ku," Tinubu ya sha alwashi kan kisan Bayin Allah a Yobe

Bola Tinubu
Jigon SDP ya soki gwamnatin Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Adewole Ebenezer ya ce Tinubu ya gaza kare rayuwar yan Najeriya kamar yadda kundin tsarin mulki ya buƙata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon SDP: 'Tinubu ya shake wuyan talaka'

Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar SDP ya ce akwai muhimmanci wajen ganin an inganta tattalin arzikin kasa kamar yadda gwamnatin tarayya ta ke ikirari.

Amma sai dai Adewole Ebenezer Adebayo ya ce ba tattalin arzikin da zai inganta ta hanyar da Bola Tinubu yake shake wuyan talakawa.

'Tinubu bai cika alkawari ba', Jigon SDP

Adewole Ebenezer Adebayo ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta gaza samar da kariya ga yan Najeriya kamar yadda kundin mulkin kasa ya buƙata.

Tribune ta wallafa cewa dan siyasar ya ce gazawar Tinubu a bayyane take wanda ko yan jam'iyyar APC za su tabbatar da hakan.

Kara karanta wannan

Malamin addini ya fadi hanyar da za a taimakawa gwamnatin Tinubu

Maganar haɗakar yan adawa a zaben 2027

Adebayo ya ce a yanzu ba maganar kayar da Tinubu a zaɓen 2027 ba ne a gabansa sabanin yadda yan adawa suke ƙoƙarin haɗaka a kai.

Ya ce yanzu haka yana son mayar da hankali ne kan yadda zai tabbatar da cewa yan Najeriya ba su shiga wahala a mulkin Tinubu ba.

NTCA ta yi magana kan zaben 2027

A wani rahoton, kun ji cewa ƙungiya mai goyon bayan shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ce shugaban zai zarce cikin sauki a zaben shekarar 2027.

Kungiyar NTCA ta yi kira na musamman ga jam'iyyun adawa da suke shirin ganin ƙarshen mulkin Bola Ahmed Tinubu a takara mai zuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng