Kungiyar NTCA Ta ce Tinubu zai Zarce a 2027, Ta ba 'Yan Najeriya Mafita

Kungiyar NTCA Ta ce Tinubu zai Zarce a 2027, Ta ba 'Yan Najeriya Mafita

  • Wata ƙungiya mai goyon bayan shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ce shugaban zai zarce cikin sauki a zaben shekarar 2027
  • Kungiyar NTCA ta yi kira na musamman ga jam'iyyun adawa da suke shirin ganin ƙarshen mulkin Bola Ahmed Tinubu a takara
  • Haka zalika ta yi kira ga 'yan Najeriya kan cigaba da yin addu'a ga shugaban kasar domin samun nasara da kawo cigaba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Wata kungiya mai goyon bayan shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi magana kan zaben shekarar 2027 mai zuwa.

NTCA ta bayyana cewa yan adawa su hakura da ganin cewa za su iya kwace mulkin Najeriya a hannun Bola Tinubu a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

“Hadama ba za ta barsu ba”: Kwankwaso kan hadakar Atiku da ’yan adawa a 2027

Bola Tinubu
Kungiyar NTCA ta bayyana yadda Tinubu zai yi nasara a 2027. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa shugaban kungiyar, Henry Nwanbueze ya yi kira na musamman ga yan Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu zai zarce a zaben 2027

Kungiyar NTCA ta ce duk masu shirin kayar da Bola Tinubu a zabe mai zuwa su ajiye shirinsu domin shugaban zai zarce.

Shugaban NTCA, Henry Nwanbueze ya ce yan siyasa su jira zuwa shekarar 2031 bayan Bola Tinubu ya yi shekaru takwas sannan su fito takara.

Kungiyar NTCA ta kawowa 'yan Najeriya mafita

Henry Nwanbueze ya ce mafita ɗaya ce ga yan Najeriya wanda ita ce yin addu'ar samun nasara ga shugaba Bola Ahmed Tinubu da Najeriya.

Ya fadi haka ne domin cewa a Najeriya ana buƙatar haɗin kai da addu'a domin samun cigaba musamman a wannan halin da ake ciki.

Masoyan Tinubu sun ce babu mafita a zanga zanga

Kara karanta wannan

Ganduje: Tinubu, Buhari da wasu ƙusoshin APC za su yanke makomar shugaban APC

Vanguard ta wallafa cewa shugaban kungiyar NTCA ya ce zanga zanga da yan Najeriya ke yi ba ita ce mafita ba.

Henry Nwanbueze ya ce zama a tattauna da gwamnati shi ne zai kawo mafita ga matsalolin da ake fuskanta a Najeriya.

2027: APC ta fitar da sabon tsari

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya fadi wasu tsare tsaren da jami'yya mai mulki ta fito da su a jihohi.

Abdullahi Umar Ganduje ya ce sun fara shirin tattara cikakkun bayanai kan yadda za su yi rajistar ƴaƴan jam'iyyar ta yanar gizo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng