An Samu Baraka, Tsagin APC Ya Caccaki Masu Goyon Bayan Ganduje
- Tsagin APC a Arewa ta Tsakiya ya ga rashin dacewar goyon bayan Abdullahi Umar Ganduje da tsohon shugaban majalisa ya yi
- Rt. Hon. Ameh Ebute ya bayyana goyon bayan Ganduje ya ci gaba da zama shugaban APC gabanin taron NEC na jam'iyyar
- A ranar 12 Satumba, 2024 ne jam'iyyar APC za ta gudanar da babban taronta na NEC, inda wasu ke fatan a canza shugaba na kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Plateau - Tsagin APC reshen Arewa ta Tsakiya ya zargi masu goyon bayan Abdullahi Umar Ganduje ya ci gaba da zama shugaban jam'iyyar da son zuciya.
Kungiyar APC ta Tsakiya karkashin jagorancin shugabanta, Saleh Zazzaga ya zargi tsohon shugaban majalisa, Ameh Ebute da son rai bisa kalamansa kan Ganduje.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Rt. Hon. Ebute ya bayyana amincewarsu da jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsagin APC ya nemi sauke Ganduje
Jaridar The Guardian ta wallafa cewa shugaban kungiyar APC a Arewa ta Tsakiya, Alhaji Saleh Zazzaga na neman a sauke Abdullahi Umar Ganduje daga mukaminsa.
Alhaji Zazzaga ya kara da cewa yanzu lokaci ne da za a mika kujerar shugaban APC na kasa ga yankin Arewa ta Tsakiya, saboda haka Ganduje bai cancanci kujerar ba.
Za a cigaba da neman sauke Ganduje
Alhaji Saleh Zazzaga ya ce ba za su daina fafutukar ganin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bar mukamin shugaban APC ba.
A sanarwar da kungiyarsa ta fitar a Jos, Alhaji Zazzaga ya ce cin amanar da ya ke zargin wasu da aikatawa ba zai hana su neman kujerar ta dawo Arewa ta Tsakiya ba.
Ganduje: An gano masu yiwa APC makarkashiya
A baya mun ruwaito cewa hadimin shugaban jam'iyyar APC na kasa, Cif Oliver Okpala ya zargi wasu yan jam'iyyar da kokarin kawo tarnaki kan kujerar Ganduje.
Cif Okpala ya bayyana cewa abin da shugaban kungiyar jam'iyyar reshen Arewa ta Tsakiya, Alhaji Saleh Zazzaga ke yi bai dace ba, kuma babu da'a a kalamansa kan Ganduje.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng