2027: Shekarau Zai Jagoranci Tawaga Mai Karfi domin Kifar da Tinubu, Sun Fara Shiri

2027: Shekarau Zai Jagoranci Tawaga Mai Karfi domin Kifar da Tinubu, Sun Fara Shiri

  • Da alamu an sake taso Shugaba Bola Tinubu a gaba a zaben 2027 inda wasu jiga-jigai a Arewacin kasar nan suka fara shiri
  • Kungiyar League of Northern Democrats da Ibrahim Shekarau yake jagoranta suna neman fadada shirinsu zuwa Kudu
  • Kungiyar ta bayyana cewa ganin yadda Tinubu ya gina siyasarsa, zai yi wahala a iya kawar da shi daga mulki cikin sauki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kungiyar League of Northern Democrats ta fara shiri kan zaben 2027 domin tumbuke Bola Tinubu a zabe.

Kungiyar wanda tsohon gwamnan Kano, Mallam Ibrahim Shekarau ke jagoranta ta fara shiri mai karfi game da zaben 2027.

Kara karanta wannan

"Akwai jan aiki a gaba": Yadda 'yan Najeriya za su magance matsalolin kasar da kansu

Shekarau sun hada tawaga domin kayar da Tinubu a 2027
Shekarau zai jagoranci hadaka mai karfi saboda zaben 2027 domin kayar da Tinubu. Hoto: @officialABAT/@mambayyahouse.
Asali: Twitter

2027: An fara shirin kifar da Tinubu

Tribune ta ruwaito cewa kungiyar an kafa ta ne domin hada kan manyan 'yan siyasar Arewa masu manufa daya da ba su cikin gwamnatin Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan gudanar da ganawar 'yan siyasar daga Arewa maso Yamma da Gabas da kuma ta Tsakiya, kungiyar na shirin fadada shirinta zuwa Kudancin kasar.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa kungiyar tana kokarin fadada shirinta ne musamman yankin Kudu maso Yamma da Tinubu ya fito.

Kungiyar ta tabbatar da cewa idan har ba a yi hadaka mai karfi ba, zai yi wahala a iya yin nasara kan Tinubu a zabe, kamar yadda The Sun ta ba da rahoto.

"Yadda Tinubu yake da karfi a siyasa da kuma samun wasu a kusa da shi da ke jam'iyyar PDP, zai yi wahalar kayarwa a zaben 2027 yadda abubuwa ke tafiya."

Kara karanta wannan

Tura ta kai bango: Ana hasashen Tinubu zai sallami wasu Ministocinsa, za a yi gyara

"Idan har mun yi tawaye da mulkin soja a Najeriya, abu mai muhimmanci shi ne hana mulkin mutum daya, yadda Tinubu ya rike abubuwa akwai barazanar komawa baya na mulkin mutum daya."

- Cewar majiyar

Ana hasashen tawagar za ta shiga har Kudancin kasar domin yin tafiya mai karfi gami da kwace mulki daga hannun Tinubu.

Shekarau ya yabawa Tinubu kan nade nade

Kun ji cewa tsohon gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau ya yi magana kan nadin shugabannin tsaro.

Shekarau ya yabawa Shugaba Bola Tinubu kan nadin shugabannin tsaro daga yankin Kudu maso Yammacin kasar.

Tsohon gwamnan ya ce kowa Tinubu ya nada a mukami idan har zai samar da abin da ake bukata abin yabawa ne.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.