Gwamna Abba Ya Sake Rusa Aikin Ganduje, Ya Maido Makarantun Kwanan Mata 15
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dawo da makarantun kwana 15 na mata waɗanda AbdullahuGanduje ya soke a zamanin mulkinsa a Kano
- Abba ya bayyana cewa tuni shirye-shirye suka yi nisa na sake mayar da makarantun na kwana kamar yadda aka sansu a baya
- Gwamnan ya faɗi haka ne a lokacin ziyara ba zata domin duha aiki a makarantar sakandiren Mata da ke ƙaramar hukumar Albasu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano ya soke matakin da tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ɗauka na canza wasu makarantun kwana 15 zuwa na jeka ka dawo.
Gwamma Abba ya ce gwamnatinsa ta maido da makarantun sakandiren guda 15 na mata zuwa matsayinsu na makarantun kwana.
Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abba ya maido da wasu makarantun kwana
Abba Kabir ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar ba zata makarantar sakandiren mata ta gwamnati da ke karamar hukumar Albasu a jihar Kano.
Gwamnan ya nuna matuƙar ɓacin ransa kan cire makarantun daga tsarin karatun kwana, inda ya ce hakan ya daƙile wasu ɗalibai mata masu hazaƙa.
Ya kuma umarci ma'aikatar ilimi ta jihar Kano ta gaggauta tura malaman lissafi, turanci da na kimiyya zuwa makarantar sakandiren mata da ke Albasu.
Gwamma Abba ya ce aiki ya yi nisa na sake maido da makarantun su koma na kwana kamar yadda aka sansu a baya.
A cewarsa, gwamnatin Kano ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen sabunta ajujuwa da gina sababbi domin samar da yanayi mai kyau na koyo da koyarwa a makarantu.
Gwamnan Kano ya yaba da aikin titin Albasu
Abba Kabir Yusuf ya kuma duba aikin gina titin zuwa Albasu mai tsawon kilomita biyar, wanda ya zu haka ake dab da kammalawa.
Gwamnan ya yaba da yadda ya ga aikin sannan ya roki ɗan kwangilar ya ƙara azama domin ƙarasa aikin cikin ƙanƙanin lokaci.
Gwamnatin Kano ta kama shugaban makaranta
Kuna da labarin gwamnatin Kano ta cafke wani shugaban makarantar firamare bisa zargin cefanar da wasu cikin kayan da aka zuba a makarantar.
Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa (PCACC) ce ta kama malamin makarantar firamaren Gaidar Makada.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng