APC Ta Samu Gagarumar Nasara a Zaben Kananan Hukumomin Jihar Kebbi

APC Ta Samu Gagarumar Nasara a Zaben Kananan Hukumomin Jihar Kebbi

  • Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Kebbi ta samu nasara a zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin da aka gudanar
  • Jam'iyyar ta lashe kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 21 da Kansiloli 25 a zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar
  • Hukumar zaɓen jihar ta sanar da sakamakon zaɓen ne wanda jam'iyyun siyasa 17 suka fafata a ranar Lahadi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kebbi - Jam’iyyar APC ta lashe dukkanin kujerun shugabannin ƙananan hukumomi 21 da Kansiloli 225 a jihar Kebbi.

A ranar Asabar ne hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kebbi (KESIEC) ta gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar.

APC ta lashe zabe a Kebbi
APC ta lashe zaben kananan hukumomi a Kebbi Hoto: Legit.ng
Asali: Original

APC ta lashe zaɓe a Kebbi

Da yake bayyana sakamakon zaɓen a Birnin Kebbi, babban birnin jihar a ranar Lahadi, shugaban KESIEC, Aliyu Muhammad-Mera, ya ce jam’iyyar APC ta lashe dukkanin kujerun, cewar rahoton jaridar The Cable.

Kara karanta wannan

Kebbi: APC ta mayar da martani bayan sanar da sakamakon zaben ƙananan hukumomi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aliyu Muhammed-Mera ya ce jam’iyyun siyasa 17 ne suka fafata a zaɓen da suka haɗa da Labour Party (LP), NNPP, Boot Party (BP), SDP da Accord Party (AP), rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Ya bayyana cewa hukumar INEC ta amince da sakamakon zaɓen na shugabannin ƙananan hukumomi da Kansiloli waɗanda jami'an zaɓen suka sanar.

Jam'iyyar PDP ta ƙi shiga zaɓen

A kwanakin baya ne jam’iyyar PDP a jihar Kebbi ta sanar da janyewa daga shiga zaɓen na ƙananan hukumomin.

Jam’iyyar ta yi zargin cewa shugaban hukumar KESIEC da kwamishinonin hukumar ƴan jam’iyyar APC ne.

PDP ta bayyana cewa ba ta da ƙwarin gwiwar cewa shugabannin zaɓen za su gudanar da zaɓen bisa gaskiya da adalci.

Jiga-jigan NNPP sun koma APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya karɓi manyan jiga-jigan jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC a hukumance.

Kara karanta wannan

NNPP ta samu koma baya a Kano, manyan jiga jiganta sun koma APC

Sanata Barau ya karɓi jiga-jigan na NNPP ne bayan sun bar tafiyar Kwankwasiyya sun dawo jam'iyyar APC mai mulki a tarayyar Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng