NNPP Ta Samu Koma Baya a Kano, Manyan Jiga Jiganta Sun Koma APC

NNPP Ta Samu Koma Baya a Kano, Manyan Jiga Jiganta Sun Koma APC

  • Jam'iyyar NNPP ta samu koma baya a Kano bayan manyan jiga-jiganta sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC mai adawa a jihar
  • Masu sauya sheƙar da suka haɗa da shugaban ƙungiyar Askarawan Kwankwasiyyya a Dawakin Tofa sun shiga APC
  • Sun bayyana salon shugabanci na mataimakin shugaban majalisar dattawan a matsayin dalilinsu na shigowa jam'iyyar APC

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya karɓi manyan jiga-jigan jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC a hukumance.

Sanata Barau Jibrin ya karɓi jiga-jigan na NNPP ne bayan sun bar tafiyar Kwankwasiyya sun dawo jam'iyyar APC.

Mambobin NNPP sun koma APC a Kano
Sanata Barau ya karbi mambobin NNPP zuwa APC Hoto: Barau I. Jibrin
Asali: Facebook

Sanata Barau ya karɓi masu sauya sheƙar ne a ranar Lahadi a gidansa da ke Abuja, kamar yadda ya sanya a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

APC ta samu gagarumar nasara a zaben kananan hukumomin jihar Kebbi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa suka bar NNPP zuwa APC?

Daga cikin fitattun waɗanda suka sauya sheƙar akwai Alhaji Bala Uba Kulkul, shugaban ƙungiyar Askarawan Kwankwasiyya a ƙaramar hukumar Dawakin Kudu da tsohon shugaban ƙaramar hukumar Bagwai, Alhaji Aminu Ibrahim Gogori.

Alhaji Bala Uba Kulkul, tare da kwamandoji 15 na Askarawan Kwankwasiyya, sun bayyana salon shugabancin Sanata Barau a matsayin dalilin da ya sa suka baro jam'iyyar NNPP.

Alhaji Bala ya bayyana ƙudirin su na marawa jam’iyyar APC baya a faɗin jihar Kano, inda suka yi alƙawarin haɗa kan kwamandojin su a dukkanin ƙananan hukumomi 44.

Alhaji Aminu Ibrahim Gogori tare da Kansiloli da wasu jiga-jigan NNPP na ƙaramar hukumar Bagwai sun bayyana rashin cika musu alƙwarin da aka yi musu a matsayin dalilinsu na ficewa daga jam'iyyar.

Sanata Barau ya yi musu maraba

Kara karanta wannan

Atiku ya haɗu da Nuhu Ribaɗu da wani sanatan APC a Abuja, hotuna sun bayyana

Sanata Barau ya yi maraba da sababbin mambobin, inda ya ba su tabbacin samun daidaito a cikin jam’iyyar APC tare da jaddada aniyar jam’iyyar na tunkarar ƙalubalen da ƙasar nan ke fuskanta.

Ya buƙaci a nuna goyon baya ga Shugaba Bola Tinubu kan ƙoƙarin da yake yi na ciyar da ƙasar nan gaba.

Ƴan APC sun koma NNPP a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya karbi sababbin tuba daga jam'iyyar APC waɗanda suka sauya sheƙa zuwa NNPP.

Gwamna Abba Kabir ya bayyana jin daɗinsa kan tarbar sababbin tuban daga jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya waɗanda suka bar tafiyar Abdullahi Umar Ganduje.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng