Wike Ya Aika Sako Mai Zafi Ga Masu Adawa da Kasancewarsa a Gwamnatin Tinubu
- Ministan babban birnin tarayya Abuja ya yi magana kan masu adawa da kasancewarsa a cikin gwamnatin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu
- Nyesom Wike ya bayyana cewa ko kaɗan bai yi nadamar kasancewa a cikin gwamnatin ba duk da yana a cikin jam'iyyar adawa ta PDP
- Wike ya kuma shawarci masu jin haushin yana yin aiki a ƙarƙashin Shugaba Tinubu da su rungumi tiransifoma bai damu ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Rivers - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan kasancewarsa cikin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Wike ya bayyana cewa bai yi nadamar aiki ƙarƙashin Shugaba Bola Tinubu ba duk da yana jam'iyyar PDP.
Me Wike ya ce kan aiki a gwamnatin Tinubu?
Ministan ya bayyana hakan ne a wajen taron jam'iyyar PDP na jihar Rivers a birnin Port Harcourt, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wike ya kuma bayyana cewa yana jin daɗin kasancewarsa a cikin gwamnati mai ci, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.
"Muna cikin gwamnati. Muna cikin gwamnatin Tinubu tsundum. Ban yi nadamar kasancewa a cikinta ba kuma zan ci gaba da kasancewa a cikinta. Duk wanda yake jin haushin hakan ya je ya rungumi tiransifoma."
- Nyesom Wike
Wike ne ɗan adawa ɗaya tilo a gwamnatin Tinubu
Wike, wanda ya kasance ɗan jam’iyyar PDP tun fara siyasarsa a shekarar 1999, shi ne ɗan adawa ɗaya tilo a majalisar ministocin Tinubu, na jam'iyyar APC.
Mutane da dama dai sun ce Wike ya samu muƙamin minista ne saboda ya ba da gudunmawa wajen rashin nasarar tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ɗan takarar jam'iyyar PDP a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
An ba Wike shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mai ba jam'iyyar PDP shawara kan harkokin shari'a, Mark Jacob, ya ba Nyesom Wike shawara.
Mark Jacob ya buƙaci ministan na birnin tarayya Abuja, da ya mutunta kansa ta hanyar ficewa daga babbar jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya.
Asali: Legit.ng