Fitaccen Mawakin Siyasa da Ya Gwangwaje Buhari da Wakoki Ya Rasu a Kano

Fitaccen Mawakin Siyasa da Ya Gwangwaje Buhari da Wakoki Ya Rasu a Kano

  • An shiga jimami bayan samun labarin rasuwar shahararren mawakin siyasa a Arewacin Najeriya tun lokacin mulkin soja
  • Marigayin mai suna Alhaji Garba Gashuwa ya rasu ne a yau Lahadi 1 ga watan Satumbar 2024 a Kano bayan fama da jinya
  • Diyar marigayin, Maryam Garba Gashuwa ta tabbatar da rasuwar mahaifin nata da safiyar yau Lahadi 1 ga watan Satumbar 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - An shiga alhini bayan sanar da rasuwar fitaccen mawakin siyasa, Alhaji Garba Gashuwa.

Marigayin da ya shahara a wakokin siyasa ya rasu a yau Lahadi 1 ga watan Satumbar 2024 a Kano.

Mawakin siyasa a Arewacin Najeriya ya rasu a Kano
Mawakin siyasa a Arewacin Najeriya, Alhaji Garba Gashuwa ya kwanta dama a Kano. Hoto: Maryam Garba.
Asali: Facebook

Kano: Mawakin siyasa a Arewa ya rasu

Kara karanta wannan

Malaman addini sun samo dabara, an nemowa Tinubu hanyoyin rage tsadar abinci

Diyar marigayin, Maryam Garba Gashuwa ta tabbatarwa Aminiya cewa mahaifin nata ya rasu a asibitin kwararru na Murtala Mohammed da ke jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maryam ta ce mahaifin nasu ya rasu yana da shekaru fiye da 70 bayan ya sha fama da jinya.

Marigayin ya rasu ya bar iyalai da dama ciki har da mata biyu da yara 11 da tulin jikoki.

Wakokin da marigayin ya yi ga shugabanni

Rahotanni sun tabbatar da cewa Gashuwa ya dade yana wakokin siyasa tun zamanin mulkin soja.

Mawakin kafin rasuwarsa, ya yi wa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari wakoki da dama a shekarun baya.

Ya kuma yi wa jam'iyyar Buhari ta ANPP waka lokacin da tsohon shugaban kasar ke neman takarar zaɓe.

Har ila yau, ya yi wa tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida waka.

Kara karanta wannan

Kwalliya ta zo da gardama: Budurwa ta sheka lahira a wajen tiyatar karin mazaunai

Rarara ya saki sabuwar wakar yabon Tinubu

Kun ji cewa yayin da 'yan Najeriya ke ci gaba da tunzura da lamarin gwamnatin kasar, musamman 'yan Arewa, fitaccen mawaki Dauda Kahutu Rarara ya saki sabuwar wakar yabon gwamnatin Bola Ahmad Tinubu.

A sabon bidiyon da Rarara ya saki, an ji yana yabawa Tinubu ta fannin tsaro, wadatar abinci da sauran ababen more rayuwa.

Wasu kuwa, suna tofin Allah shi kara bisa ga yadda mawakin ke azarbabi wajen yaba gwamnatin da wasu ke ganin ta daure marar 'yan kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.