Tura Ta Kai Bango: Ana Hasashen Tinubu Zai Sallami Wasu Ministocinsa, Za a yi Gyara

Tura Ta Kai Bango: Ana Hasashen Tinubu Zai Sallami Wasu Ministocinsa, Za a yi Gyara

  • Da alamu tura ta kai bango yayin da ake hasashen Shugaba Bola Tinubu ya shirya yin garambawul a mukaman Ministocinsa a Najeriya
  • An ruwaito shugaban zai yi haka ne saboda yadda wasu daga Ministocinsa ba su tabuka komai da zai kawo sauyi da cigaban kasar ba
  • Duk da ba a bayyana sunayen wadanda ake tunanin sauyawa ba amma mutane da dama na yawan korafi kan wasu daga Ministocin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Ana hasashen Shugaba Bola Tinubu zai sallami wasu Ministoci da dama saboda rashin tabuka wani abu.

Rahotanni sun bayyana cewa Tinubu zai yi garanbawul din ne yayin da ake ta cece-kuce kan wasu Ministocinsa da ya nada.

Kara karanta wannan

"Akwai jan aiki a gaba": Yadda 'yan Najeriya za su magance matsalolin kasar da kansu

Tinubu ka iya sallamar da yawa daga cikin Ministocinsa a Najeriya
Ana hasashen Tinubu zai kori wasu Ministocinsa tare da sauyawa wasu ma'aikatu. Hoto: @DOlusegun.
Asali: Twitter

Tinubu zai iya korar wasu Ministocinsa

Punch ta tattaro cewa Tinubu na cigaba da samun matsin lamba daga jam'iyyar APC da kuma sauran mutane kan korar wasu Ministoci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba shugaban zai yi garambawul na wasu mukamai, cewar The Guardian.

Wani da ya bukaci boye sunansa ya ce za a kori wasu yayin da za a sauyawa wasu ma'aikatu, sai dai kuma bai bayyana Ministocin da ake magana a kansu ba saboda gudun abin da ka iya zuwa ya dawo.

"Ina mai tabbatar maka wasu Ministoci za su tafi, za a sauyawa wasu ma'aikatu yayin da wasu sababbi za su samu shiga gwamnati."
"Shugaba Tinubu ya mayar da hankali ne wurin kwarewa da kuma mutane da za su kawo sauyi a kasar da kuma cigaban al'umma."

Kara karanta wannan

Malaman addini sun samo dabara, an nemowa Tinubu hanyoyin rage tsadar abinci

- Cewar majiyar

Ana hurawa Tinubu wuta kan Ministocinsa

Har ila yau, wata majiya ta ce na kusa da shugaban sun bukaci Tinubu ya samu mukarrabai masu karfi da kuma kwarewa domin kawo cigaba.

Majiyar ta ce hadiman shugaban da abokai da kuma al'umma sun damu ganin yadda ya tara mukarrabai da ba za su iya kawo sauyi ba.

Sule ya fadi gwagwarmayar Tinubu a siyasa

Kun ji cewa tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido ya ce Shugaba Bola Tinubu ya tsallake dukan matsaloli da kalubale kafin zama shugaba.

Lamido ya ce ganin yadda Tinubu ya kama kasa zai yi wahala ga jam'iyyun adawa su iya tabuka wani abu wurin tuge shi a zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.