"Sai an dage": Sule Lamido ya yi magana kan yiwuwar kifar da Tinubu a 2027
- Tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido ya bayyana wahalar da jam'iyun adawa za su sha a zaɓen 2027
- Lamido ya ce kayar da Bola Tinubu a zaben ba karamin kalubale ba ne duba da yadda ya kafa kansa a siyasar kasar
- Ya ce Tinubu ya sha gwagwarmaya a siyasa inda ya yi nasara kan Buhari duk da bai goyon bayansa a babban taron APC ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya yi magana kan zaben 2027 da ke tafe.
Lamido ya ce ba karamin wahala zai yi ga jam'iyyun adawa su iya tumbuke Tinubu a zaben 2027 da ake tunkara ba.
Tinubu: Sule Lamido ya yi magana kan zabe
Tsohon Ministan ya bayyana haka ne yayin hira da jaridar Tribune da aka wallafa a yau Asabar 31 ga watan Agustan 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamido ya bayyana Tinubu a matsayin wanda ya kware ya kuma karanci siyasar kasar da bai dogara da kowa wurin zamowa shugaban kasa ba.
Ya ce ganin yadda ya rike mudafun iko da irin shirka da ya yi kafin samun damar yana da matukar wahala a iya kayar da shi a 2027, Vanguard ta tattaro.
"Tinubu ya yi gwagwarmaya a siyasa" - Lamido
"Zai yi matukar wahala a kayar da Tinubu ganin yadda ya rike kasar da kuma ta fannin tattalin arziki."
"Ka duba yadda ya yi gwagwarmaya a baya da yakar Obasanjo da Afenifere da kuma jam'iyyar AD."
"A lokacin babban taron APC, Buhari bai tare da shi amma ya yi nasara kansa, kada ka yi wasa da irin wannan mutumin ya sha gwagwarmaya tare da yin nasara."
Sule Lamido ya fadi matsalar Najeriya
Kun ji cewa Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya bayyana cewa kundin tsarin mulki ba shi ne matsalar Najeriya ba.
Sule Lamido ya bayyana cewa matsalar Najeriya ta samo asali ne daga shugabanninta.
Sule Lamido ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga kiran da ƙungiyar The Patriots, waɗanda suka ziyarci Shugaba Bola Tinubu tare da yin kiran a yi sabon kundin tsarin mulki
Asali: Legit.ng