Zargin N432bn: Nasir El Rufai Ya Fadi Babbar Matsalar Cigaban Siyasa

Zargin N432bn: Nasir El Rufai Ya Fadi Babbar Matsalar Cigaban Siyasa

  • Tsohon Ministan Abuja, Mallam Nasir El-Rufai ya koka kan yadda hassada da kyashi suka yi katutu a tsakanin yan siyasa
  • El-Rufai wanda tsohon gwamnan Kaduna ne ya ce yana kokwanto samun waraka kan cutar hassada da kyashi a tsakanin yan siyasa
  • El-Rufai ya yi martanin yayin da ake cigaba da zargin gwamnatinsa da almundahanar makudan kudade har N432bn

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi magana kan hassada tsakanin yan siyasa.

El-Rufai ya fadi haka ne a daidai lokacin da ake zargin gwamnatinsa da almundahana da dukiyar al'umma.

El-Rufai ya fadi illar hassada da kyashi a tsakanin yan siyasa
Nasir El-Rufai ya koka kan yadda hassada da kyashi suka yi yawa a tsakanin yan siyasa. Hoto: @elrufai.
Asali: Twitter

El-Rufai ya koka kan hassada a siyasa

Kara karanta wannan

An tono abin da shugaban kwadago ya fada wa yan sanda da suka gayyace shi

Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne a wani dogon rubutu da ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

El-Rufai ya bayyana hassada a tsakanin yan siyasa a matsayin wata cuta da ba za a iya warkewa ba.

Ya ce mafi yawan yan siyasa suna da wannan matsalar wanda ake ganin sai daya ya fadi kafin daya ya samu cigaba.

"Hassada da kyashi sun yi yawa a tsakanin yan siyasa, kwarewa da dagewa kan lamari da sanin siyasa ke jawo a yi maka hassada daga wadanda suka rasa wannan matsayi."
"Madadin neman hanyar cigaba daga ɓangarensu, sun gwammace su lalata nasarar wadanda suka samu cigaba."
"Tabbas ina kokwanton samun waraka kan wannan cuta ta hassada da kyashi tsananin yan siyasarmu."

- Nasir El-Rufai

Zargin almundahana da ake yi wa El-Rufai

Wannan martani bai rasa nasaba da zargin gwamnatinsa da ta shafe shekaru takwas kan mukin jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Likitoci sun fadi abin da ke korarsu zuwa neman aiki a kasashen waje

Ana zargin gwamnatin El-Rufai daga 2015 zuwa 2023 da almundahanar makudan kudi har N432bn.

A farkon watan Yunin 2024 ne kwamitin da aka kafa domin binciken badakalar ta mika rahotonta ga Majalisar jihar.

Ana zargin hadimin El-Rufai a Kaduna

A wani labarin, kun ji cewa tsohon hadimin Mallam Nasir El-Rufai ya shiga tarkon hukumar yaki da cin hanci ta ICPC.

Wanda ake zargin, Mr. Jimi Lawal ya samu gayyatar hukumar ICPC domin amsa tambayoyi kan zargin badakalar N11bn.

An gayyaci Lawal ne a ranar Litinin 12 ga watan Agustan 2024 amma ya ki halartar zaman kuma bai tura wani wakili ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.