Jam’iyyar APC Ta Yi Magana kan Zargin Shirin Korar Ganduje daga Mukaminsa

Jam’iyyar APC Ta Yi Magana kan Zargin Shirin Korar Ganduje daga Mukaminsa

  • Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta karyata jita-jitar shirin sallamar shugabanta, Abdullahi Ganduje daga mukaminsa
  • APC ta nuna kwarin guiwarta ga shugabancin Ganduje tare da godiya da Shugaba Bola Tinubu kan ba shi dukan goyon baya
  • Wannan na zuwa ne bayan zargin shirin jam'iyyar na tuge Ganduje daga mukaminsa a yayin taron masu ruwa da tsaki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta yi karin haske kan rade-radin tube Abdullahi Ganduje daga mukaminsa.

Jam'iyyar ta ce babu batun tuge Ganduje daga shugabancin APC bayan ganawar masu ruwa da tsakinta.

APC ta karyata shirin tube Ganduje daga shugabancinta
Jam’iyyar APC ta karyata jita-jitar cire Abdullahi Ganduje daga mukaminsa. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

APC ta yi magana game da Ganduje

Sakataren jam'iyyar na kasa, Sanata Ajibola Basiru shi ya bayyana haka bayan ganawa da kwamitin gudanarwa, cewar The Guardian.

Kara karanta wannan

"Za mu saka kafar wando daya da ku": Majalisar Tarayya ta ja kunnen al'umma

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Basiru ya ce babu wani shiri na tuge Ganduje bayan ganawar inda ya ce sun gabatar da rahoto kan ayyukan jam'iyyar.

Sanatan har ila yau, ya godewa Shugaba Bola Tinubu kan irin goyon baya da yake ba Abdullahi Ganduje. The Nation ta tattaro.

Ganduje ya samu goyon bayan shugabannin APC

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Gwamna Abdullah Sule na jihar Nassarawa da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya.

Sule ya nuna kwarin guiwarsa kan shugabancin Ganduje inda ya bukaci hadin kai domin lashe zabukan jihohin Edo da Ondo da ake tunkara a 'yan kwanakin nan.

Gwamnan ya ce duba da abubuwan da ke faruwa a cikin APC, bai kamata ƴaƴam jam'iyyar su takurawa Ganduje da sauran ƴan kwamitin NWC ba.

Ana hasashen Tinubu zai sauyawa Ganduje mukami

Kara karanta wannan

Malaman addini sun samo dabara, an nemowa Tinubu hanyoyin rage tsadar abinci

Kun ji cewa ana hasashen Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai iya sauyawa shugaban jam'iyyar APC, Dakta Abdullahi Umar Ganduje mukami.

Rahotanni sun bayyana cewa shugaban zai iya mayar da Ganduje a matsayin jakada a kowace kasa da ke Nahiyar Afirka inda ya ba shi zabi a cikinsu.

Wata majiya da ta bukaci boye sunanta ta ce farko an tura shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio domin ya sanar da Ganduje shirin Tinubu kan haka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.