Kano: Abba Kabir Ya Karbi Daruruwan 'Yan APC Kwanaki Kadan da Barau Yayi Masa Illa

Kano: Abba Kabir Ya Karbi Daruruwan 'Yan APC Kwanaki Kadan da Barau Yayi Masa Illa

  • A yau Juma'a 30 ga watan Agustan 2024, Gwamna Abba Kabir ya karbi wasu magoya bayan jam'iyyar APC zuwa NNPP
  • Gwamna Abba ya nuna farin cikinsa kan sauya shekar da 'yan APC suka yi zuwa jam'iyyar NNPP mai mukin jihar
  • Hakan na zuwa ne yayin da wasu daga mambobin NNPP da dama suka koma jam'iyyar APC a kwanakin baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya karbi sababbin tuba daga jam'iyyar APC zuwa NNPP.

Abba Kabir ya ba bayyana jin dadinsa kan tarbar sababbin tuban daga jam'iyya mai mulkin kasar.

Abba Kabir ya karbi sababbin tuba daga APC zuwa NNPP a Kano
Gwamna Abba Kabir ya nuna farin cikinsa bayan karbar mambobin APC zuwa NNPP. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Asali: Facebook

Kano: Gwamna Abba ya karbi mambobin APC

Gwamnan ya tabbatar da haka ne a yau Juma'a 30 ga watan Agustan 2024 a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban PDP kuma sanata ya jefar da jam'iyyar, ya yi mata bazata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanda suka watsar da jam'iyyarsu ta APC zuwa NNPP sun fito ne daga karamar hukumar Ghari a jihar.

Abba Kabir ya kuma bayyana cewa ya ziyarci duba aikin gyaran Kwalejin Ilimi da ke karamar hukumar Ghari.

Abba ya kaddamar da hanya a Ghari

"Na wuni a Kano ta Arewa inda na kai ziyarar gani da ido game da gyaran Kwalejin Ilimi da ke karamar hukumar Ghari."
"Za a fara daukar dalibai nan ba da jimawa ba, na kuma duba aikin hanya mai tsawon kilomita biyar a wanda ban ji dadin yadda aikin ke tafiya ba, na ba dan kwangilar mako daya ya dawo aiki ko kuma na kwace kwangilar tare da ba wani kamfani."
"Mun kuma kaddamar da hanyar Titin 'Yan Dadi a Ghari da kuma karbar mambobin APC 500 da suka dawo jam'iyyar NNPP."

Kara karanta wannan

Tafiyar Kwankwasiyya ta samu matsala a Kano, fiye da mutane 6000 sun sauya sheka

- Abba Kabir Yusuf

Sanata Barau ya karbi dubban 'yan NNPP

Kun ji cewa Mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibirin ya karbi 'yan kungiyar 'Na Dikko Dakin Kara' da suka koma jam'iyyar APC.

Kungiyar 'yan asalin Katsina mazauna Kano bisa jagorancin Alhaji Usman Abdullahi Masari sun sanar da ficewarsu daga tafiyar Kwankwasiyya.

Bayan karbar sababbin tuban, Sanata Barau ya jinjina masu kan wannan tunani da suka yi na komawa APC inda ya yi alkawarin ba su kulawa kamar kowa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.