Zaben 2027: Kalu Ya Bayyana Mutum 1 da Zai Iya Kwace Mulki daga Hannun Tinubu

Zaben 2027: Kalu Ya Bayyana Mutum 1 da Zai Iya Kwace Mulki daga Hannun Tinubu

  • An bayyana Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa a matsayin mutum daya tilo da zai iya kwace mulki daga APC
  • Shugaban kungiyar GIGG, Dakta Emeka Kalu ya ce a halin da ake ciki, Najeriya na bukatar mutum kamar Atiku matsayin shugaba
  • Bayanin Dakta Kalu martani ne ga jigon PDP, Olabode Geroge wanda ya ce Atiku ba zai iya cin zaben 2027 ba sai dai ya jira 2031

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban kungiyar GIGG, Dakta Emeka Kalu ya ce tsohon mataimakin shugaban Najeriya ne kadai zai iya kwace mulki daga hannun APC a 2027.

Dakta Kalu ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga Olabode Geroge, jigon jam'iyyar PDP wanda ya ce dole Atiku ya jira 2031 kafin ya ci zabe.

Kara karanta wannan

Ajuri Ngelale, Lalong da sauran mutum 5 da suka ajiye mukamai a gwamnatin Tinubu

Dakta Emeka Kalu ya yi magana kan tasirin Atiku a zaben 2027
Shugaban GIGG ya bayyana Atiku matsayin wanda zai iya karbar mulki daga APC. Hoto: @atiku, @officialABAT
Asali: Twitter

Kalu ya yabi halayen Atiku Abubakar

Jaridar The Sun ta ruwaito Dakta Kalu ya bayyana cewa shugabanci wani al'amari ne mai wuyar sha'ani wanda ya ke bukatar kwarewa irin ta Atiku.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban GIGG ya ce Atiku ya kasance mutum wanda ko kadan ba ruwansa da nuna wariya, kuma shi ne ke da abokai daga kowane bangare na kasar.

Ya kalubalanci wadanda ke adawa da takarar Atiku yana mai cewa su ne wadanda ba sa son jagora na kwarai ya hau kan madafun iko saboda wata manufa, inji rahoton Vanguard.

"Atiku zai gyara Najeriya" - Kalu

Dakta Kalu ya ce:

“Yayin da zaben 2027 ke karatowa, Atiku Abubakar ne mutum daya tilo da ke da kwarewar da zai iya gyara Najeriya tare da farfado da tattalin arzikin kasar.
"A halin da kasar nan ke ciki yanzu, akwai bukatar a zabi shugaban da zai hada kan jama'a da kuma gyara barnar da gwamnatin APC ta yi a shekarun da ta yi."

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban PDP kuma sanata ya jefar da jam'iyyar, ya yi mata bazata

Dakta Kalu ya dage kan cewa idan Atiku ne shugaban kasa, Najeriya za ta samu ci gaba ta fuskar tattalin arziki,zuba jari, kayayyakin more rayuwa da tsaron rayuka da dukiyoyi.

Timi Frank ya tarewa Atiku fada

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon mataimakin kakakin jam'iyyar APC na kasa, Mista Timi Frank ya tarewa Atiku Abubakar fadan da ake yi da shi.

Timi Frank ya yiwa jigon PDP, Olabode Geroge martani kan cewa tsohon mataimakin shugaban kasar ba zai ci zaben 2027 ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.