"Arewa Ta Yi Hakuri," Sanatan Kaduna Ya Faɗi Wanda Ya Kamata Mutane Su Zaɓa a 2027
- Shehu Sani ya bayyana cewa kamata ya yi Arewa ta hakura ta bar ƴan Kudu su ci gaba da mulkin Najeriya a babban zaɓen 2027
- Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya ya ce daga nan kuma Arewa za ta samu cikakkiyar damar samar da shugaban ƙasa a 2031
- Ya ƙara da cewa Bola Tinubu ya cancanci ya kara samun goyon bayan ƴan Arewa saboda abin da ya yi masu lokacin zaben 2015
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna - Tsohon sanatan Kaduna da tsakiya, Shehu Sani ya tsoma baki kan muhawarar da ake ta yi kan tazarcen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a 2027.
A cewar Shehu Sani, kundin tsarin mulkin kasa ya bai wa kowane dan Najeriya damar tsayawa takara kuma ko daga wane yanki ya fito.
Sanatan ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da wakilin jaridar Punch a Kaduna ranar Alhamis, 29 ga watan Agusta, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shehu Sani ya faɗi ra'ayinsa kan zaɓen 2027
Ya ƙara da cewa kamata ya yi a bar ƴan Kudancin Najeriya su sake neman takara a 2027, wanda hakan zai ba Arewa damar samar da shugaban ƙasa a 2031.
Sanata Shehu Sani ya ce:
"A nawa ra'ayin, kamata ya yi a bar ƴan Kudu su ci gaba da mulki a 2027, ko shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya yi tazarce, ko Peter Obi ko tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan."
"Daga nan kuma Arewa zata samu cikakkiyar damar samar da shugaban ƙasa na gaba a 2031," in ji Shehu Sani.
'Dalilin Arewa na sake zaɓen Tinubu'
Sai dai tsohon sanatan ya ƙara da cewa zai fi kyau Arewa ta marawa Shugaba Tinubu baya fiye da kowane ɗan Kudu saboda shi ne mutum ɗaya tilo da ya tsaya masu.
Tsohon sanatan kuma jigo a PDP ya ce tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya nemi takara sau da dama amma bai yi nasara ba sai da ya haɗe da Tinubu.
Sanata Shehu Sani ya shawarci gwamnatin Bola Tinubu ta maida hankali wajen magance matsalar tsaro, fatara da jahilci a Arewa saboda a sake zaɓensa a 2027.
Ya kuma kara da cewa kwadayin da wasu jiga-jigan siyasar Arewa suke yi na kwace mulki bai dace da ra'ayin ƴan Arewa ba illa dai wasu dalilai ne na kashin kansu, rahoton Vanguard.
Da wahala ƴan Arewa su yi Tinubu
Wasu ƴan Arewa sun shaidawa Legit Hausa cewa ba za su sake zaɓen Bola Tinubu ba domin a yanzu ma sun fara nadamar goyon bayan da suka ba shi.
Abdulhafiz Abdullahi ya ce duk idan ya tuna cewa Tinubu ya zaɓa ya kan ji nadama da takaici saboda halin ƙuncin da ake ciki.
"Duk yadda muka tsani Buhari daga ƙarshe ashe gara shi, wallahi mutane suna cikin wahala, ni dai a karan kaina ba zan ƙara zaɓen Tinub ba," in ji shi.
Haka nan wani ɗan APC a Katsina, Usman Ahmad ya ce ya yi wuri a fara magana kan wanda ya kamata a zaɓa a 2027.
APC na shirin ƙwace jihohin Najeriya
A wani rahoton kuma shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa jam'iyyar na shirin ganin jihohin Najeriya 36 sun dawo hannunta.
Ganduje ya nuna ƙwarin gwiwar cewa APC za ta lashe zaɓukan gwamna a jihar Ondo da Edo waɗanda za a yi a wannan shekarar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng