Abba Ya Samu Giɓi Ana Shirin Zabe, Shugabannin Kwankwasiyya Sun Koma APC
- Yan Kwankwasiyya da dama a jihar Kano sun sauya sheƙa zuwa APC mai mulki ana maganar zaben kananan hukumomi
- An samu jiga jigan jam'iyyun PDP da SDP da suka sauya sheƙa zuwa APC ta hannun mataimakin shugaban majalisar dattawa
- Sanata Barau Jibrin ne ya karbi yan siyasar da suka sauya shekar kuma ya musu alkawari kan yadda za su cigaba da tafiya tare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Yayin da aka fara maganar sayar da fom din takara domin zaben kananan hukumomi a Kano, siyasa ta fara daukan sabon salo.
Wasu yan jam'iyyun NNPP, PDP da SDP sun sanar da komawa jami'yyar APC mai mulki a Najeriya.
Legit ta tattaro bayanai kan lamarin ne a cikin sakon da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan NNPP sun koma APC a Kano
Sanata Barau Jibrin ya wallafa cewa wasu daga cikin shugabannin Kwankwasiyya sun fice daga tafiyar gwamna Abba Kabir Yusuf.
Mutanen sun hada da shugabannin Kwankwasiyya Movement daga karamar hukumar Kunchi da shugabannin Kwankwasiyya Salama.
Kano: Yan PDP da SDP sun koma APC
Haka zalika Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa ya karbi tsohon shugaban kungiyar kansilolin PDP a jihar.
A daya bangaren, mataimakin dan takarar gwamna a SDP, Sabo Habibu Dundu ya koma jam'iyyar APC.
Barau ya yi godiya ga mutanen Kunci
Sanata Barau Jibrin ya mika godiya ga mutanen ƙaramar hukumar Kunci bisa goyon baya da suke nuna masa tun a baya.
Barau Jibrin ya tabbatar musu da cewa za su yi aiki tare domin kawo cigaba a bangarori da dama a jihar Kano.
Alin Kano ya koma jam'iyyar APC
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Barau I Jibrin ya karɓi ɗaya daga cikin kusoshin jam'iyyar PDP a jihar Kano wanda aka fi sani da Alin Kano zuwa APC.
Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya ce sauya sheƙar fitaccen ɗan siyasar zai ƙarawa APC karfi a Kano da ƙasa baki ɗaya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng