Tsohon Mataimakin Shugaban PDP Ya Jiƙawa Atiku Aiki Game da Takara a 2027
- Bode George ya bayyana cewa Atiku Abubakar ba zai samu tikitin takarar shugaban ƙasa a 2027 ba sai dai ya jira 2031
- Tsohon shugaban na PDP ya ce a hankalce da kuma kundin tsarin mulkin jam'iyyarsu, mulki zai ci gaba da zama a kudu
- A cewarsa, tsohon shugaba Muhammadu Buhari, ɗan Arewa ya shafe shekaru takwas a mulki don haka yanzu lokacin kudu ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Tsohon mataimakin shugaban PDP, Cif Bode George ya ce dole Atiku Abubakar ya jira 2031 idan yana son sake neman zama shugaban ƙasa.
Idan ba ku manta ba Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2023, ya sha kaye a hannun shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na APC.
A wata sanarwa da ya fitar yau Laraba, Bode George ya ce ya zama dole Kudu ta ci gaba da mulki har zuwa 2031, kamar yadda The Nation ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ya kamata Atiku ya hakura da takara"
Bode George ya ƙara da cewa a 2027, Alhaji Atiku zai cika shekara 81 a duniya, inda ya ce ya kamata ya yi koyi da Shugaba Joe Biden na Amurka, ya haƙura ya bar wa matasa.
"Ko a 2027, Atiku zai cika shekaru 81, ya kamata ya yi koyi da Shugaba Joe Biden na ƙasar Amurka, ya ba matasa damar tsayawa takarar kujera lamba ɗaya a ƙasar nan.
"Ba ni da wata matsala da Atiku, abokina ne amma ita gaskiya ɗaya ce dole mu faɗe ta, ni kaina a 2027 zan cika shekara 80 a duniya, shekaru sun ja, wane abu kuma zan nema?"
- Cif Bode Gearge.
Abin da zai hana da Atiku takara a 2027
A cewarsa, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, dan asalin jihar Katsina a Arewacin Najeriya, ya sauka daga mulki ne bayan ya shafe shekaru takwas.
George ya ce mulki ba zai koma Arewa a 2027 ba saboda haka ne gaskiya kuma haka jam'iyyar PDP ta tanada a kundin tsarin mulkinta, cewar rahoton Punch.
Sakamakon haka ne tsohon mataimakin shugaban PDP ya ce ba zai yiwu Atiku ya nemi takara a 2027 ba, sai dai ya jira zuwan 2031.
Bwala ya ɗora laifin tsaro kan yan siyasa
A wani rahoton kuma Daniel Bwala ya yi ikirarin cewa manyan ƴan siyasar da suka sha kashi a zaɓen 2023 suna da hannu a taɓarɓarewar tsaron Najeriya.
Tsohon kakamin kamfen Atiku/Okowa 2023 ya nuna goyo baya ga kalaman tsohuwar minista da ta ce rashin tsaro ya zama makamin ƴan siyasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng