Tsohon Kakakin Kamfen Atiku Ya Faɗi Ƴan Siyasar da Ke Rura Wutar Rashin Tsaro a Najeriya

Tsohon Kakakin Kamfen Atiku Ya Faɗi Ƴan Siyasar da Ke Rura Wutar Rashin Tsaro a Najeriya

  • Daniel Bwala ya yi ikirarin cewa manyan ƴan siyasar da suka sha kashi a zaɓen 2023 suna da hannu a taɓarɓarewar tsaron Najeriya
  • Tsohon kakamin kamfen Atiku/Okowa 2023 ya nuna goyo baya ga kalaman tsohuwar minista da ta ce rashin tsaro ya zama makamin ƴan siyasa
  • Bwala ya lura cewa zanga zangar da aka yi kwanan nan wani makirci ne na masu kokarin kawar da gwamnati mai ci daga karagar mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon kakakin kwamitin kamfen Atiku Abubakar a zaɓen 2023, Daniel Bwala ya ce wasu manyan ƴan siyasar ƙasar nan suna da hannu a matsalar tsaro.

Fitaccen ɗan siyasar ya bayyana cewa zanga-zangar da aka yi da sunan adawa da yunwa an fake ne da guzuma, amma wani yunkuri ne na kifar da gwamnati mai ci.

Kara karanta wannan

Ana fama da yunwa, ambaliyar ruwa ta yi ɓarna a gonakin mutane a jihohi 2 na Arewa

Bola Tinubu da Bwala.
Bwala ya zargi ƴan siyasa da hannu a rura wutar matsalar tsaro a Najeriya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Daniel Bwala
Asali: Twitter

Meyasa Bwala ke zargin ƴan siyasa?

Bwala ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a cikin shirin siyasa a yau na gidan talabijin na Channels tv ranar Talata, 27 ga watan Agusta, 2027.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi wannan furucin ne da yake tsokaci kan kalaman tsohuwar ministar kuɗi, Ngozi Okonjo-Iweala, wanda ta fito fili ta ce ƴan siyasa na amfani da matsalar tsaro a matsayin makami.

Daniel Bwala ya ce ya amince da kalaman Okonjo-Iweala, yana mai cewa wadanda suka fadi zabe su ne ke ƙara ruwa wutar rashin tsaro a Najeriya.

Tsohon jigon PDP ya magantu kan tsaro

A rahoton Daily Trust, Bwala ya ce:

"Ku duba zanga-zangar da aka jinginawa matasa, wasu ne fa kawai suka so ƙwace mulki, muna da mutane a lungu da saƙon ƙasar nan.
"Galibin mutane ba su iya gane tutocin kasashen waje ba amma aka riƙa ɗinka tutocin Rasha tare da rera waka, ana rokon Rasha ta zo ta karbe kasar domin sojoji su karbi gwamnati.

Kara karanta wannan

Sunayen gwamnonin Arewa da ake zargin sun kitsa zanga zangar adawa da Tinubu, Rahoto

“Yan siyasa na da hannu a kan lamarin. Batun da (Okonjo Iweala) ta yi ba ɓoyayyen abu ba ne. Ku dubi yanayin da Najeriya ke ciki, kullum a haka muke."

Lukman ya hango faɗuwar ƴan adawa a 2027

A wani rahoton kuma Salihu Lukman ya bayyana cewa kwaɗayin mulki ba zai bar shugabannin adawa su taɓuka komai ba a zaben 2023 ba.

Tsohon jigon APC ya ce dukkan manyan jam'iyyun adawa suna fama da rikicin cikin gida da faɗa da juna kan abin da bai taka kara ya .karya ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262