Zargin Rashin Turanci: An Garkame Hadimin Sanata Tambuwal kan Sukar Gwamna

Zargin Rashin Turanci: An Garkame Hadimin Sanata Tambuwal kan Sukar Gwamna

  • An tunkuda keyar hadimin Sanata Aminu Waziri Tambuwal a gidan yari bayan cin zarafin Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto
  • An cafke Shafi'u Tureta ne a ranar 25 ga watan Agusta bayan yada bidiyo da ke nuna gwamnan na kokarin hada kalmomin Turanci da kyar
  • Daga bisani kotun ta dage cigaba da sauraran karar har zuwa ranar 6 ga watan Satumbar 2024 domin daukar matakin da ya dace a kansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Rundunar yan sanda a jihar Sokoto ta gurfanar da hadimin Sanata Aminu Tambuwal kan cin zarafin gwamnan jihar.

Ana zargin Shafi'u Tureta da cin mutuncin Gwamna Ahmed Aliyu inda ya wallafa faifan bidiyo da cewa bai iya yaren Turanci ba ko kadan.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi artabu da miyagu, an sheke 'yan bindiga a Katsina

An cafke hadimin Tambuwal kan cin mutuncin gwamnan Sokoto
An tasa keyar hadimin Sanata Tambuwal gidan kaso kan cin mutuncin Gwamna Ahmed Aliyu na Sokoto. Hoto: Aminu Waziri Tambuwal, Ahmed Aliyu.
Asali: Facebook

An cafke hadimin Sanata Tambuwal

Punch ta tattaro cewa Tureta ya kuma yada takardar sakamakon gwamnan na sakandare da cewa yayi mummunan faduwa a wasu darusa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gurfanar da Tureta ne a gaban kotun Majistare da ke jihar tun a ranar 25 ga watan Agustan 2024 da cewa ya aikata laifi wanda ya saba doka.

Premium Times ta ruwaito cewa ana kuma zargin Tureta da yada bidiyon matar gwamnan, Hajiya Fatima Aliyu da watsa kudi a biki duk da halin kunci da ake ciki.

Sokoto: Lauyan wanda ake zargi ya magantu

Lauyan wanda ake zargi, Al-Mustapha Abubakar ya fadawa yan jaridu cewa Tureta ya musanta aikata laifin inda ya bukaci ba shi beli.

Al-Mustapha ya ce kotun ta dage sauraran shari'ar zuwa ranar 6 ga watan Satumbar 2024 inda ta garkame Tureta a gidan gyaran hali.

Kara karanta wannan

Kaduna: Yan bindiga sun shammaci kauye cikin dare, sun sace basarake da 'yarsa

Tambuwal ya tafka babban rashi a Sokoto

Kun ji cewa Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya yi jimamin mutuwar kaninsa mai suna Alhaji Ahmed Ibrahim Tambuwal a jihar Sokoto.

Marigayin ya rasu ne a ranar Asabar 24 ga watan Agustan 2024 a Abuja bayan ya sha fama da jinya inda aka yi sallar jana'izarsa a Sokoto.

Sanata Tambuwal ya ce marigayin ya wuce dan uwa kawai, ya zama abokinsa kuma wanda ya aminta da shi matuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.