Rikicin APC Ya Dauki Zafi Bayan an Dakatar da Shugabannin Jam'iyya
- Shugabannin APC da ke tsagin Ugochukwu Agballah a jihar Enugu sun dakatar da wasu mambobi na jam'iyyar
- Shugabannin sun dakatar da mambobi 20 na tsagin Alphonus Nwafor bayan sun dakatar da Agballah a kwanakin baya
- Uwar jam'iyyar APC ta ƙasa ƙarƙashin jagorancin Abdullahi Ganduje ta ce Agballah ta sani a matsayin shugaban
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Enugu - Rikicin shugabancin jam'iyyar APC a jihar Enugu ya ƙara ɗaukar zafi.
Tsagin da ke ƙarƙashin jagorancin Ugochukwu Agballah ya sanar da dakatar mambobi 20 bisa zarginsu da rashin da biyayya da yiwa kundin tsarin mulkin jam'iyyar hawan ƙawara.
Hakan ya biyo bayan dakatar da Ugochukwu Agballah da wasu shugabannin jam'iyyar da tsagin APC ƙarƙashin Alphonus Nwafor ya yi a kwanakin baya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jagororin jam'iyyar APC sun zauna a Enugu
A wajen taron masu ruwa da tsaki da aka yi a sakatariyar jam'iyyar ranar Asabar, tsagin da Agballah ke jagoranta ya sanar da dakatar da dukkanin mambobin da ke tsagin Alphonus Nwafor, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Taron ya samu halartar mataimakin shugaban jam'iyyar APC na ƙasa (yankin Kudu), Cif Emma Eneukwu, ministan kimiyya da fasaha, Cif Uche Nnaji, Sanata Chukwuka Utazi, Ugochukwu Agballah da sauransu.
Wanene Ganduje yake goyon baya a APC?
Cif Emma Eneukwu, wanda ya wakilci shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa har yanzu Ugochukwu Agballah ne shugaban APC a jihar.
Ya bayyana cewa uwar jam'iyyar ta ƙasa ba ta da masaniya kan cire Agballah daga muƙaminsa, inda ya nanata cewa cire shin da aka yi, ba a aiwatar bisa tsarin doka ba.
A sanarwar bayan taron da Sanata Chukwuka Utazi ya karanta, sun sanar da dakatar da mambobin 20 da suka haɗa da Alphonus Nwafor da wasu daga cikin mambobin kwamitin gudanarwa na jihar.
Jigon APC ya caccaki Bola Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa jigon jam'iyyar APC kuma na hannun daman tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya yi magana kan yiwuwar tazarcen Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Cif Eze Chukwuemeka Eze ya bayyana cewa yunwar da ƴan Najeriya ke ciki ita za ta sanya su yi waje da Shugaba Tinubu daga kan kujerar mulkin ƙasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng