Zaben Fitar da Gwani: Sabuwar Matsala Ta Kunno Kai a Jam’iyyar APC, Bayanai Sun Fito

Zaben Fitar da Gwani: Sabuwar Matsala Ta Kunno Kai a Jam’iyyar APC, Bayanai Sun Fito

  • Sabon rikicin cikin gida ya barke a APC reshen jihar Binuwai kan zaben fitar da gwani da wani tsagin jam'iyyar ya gudanar makon baya
  • A halin yanzu dai kwamitin gudanarwar APC karkashin Benjamin Omale da na bangaren Austin Agada sun fara nunawa juna yatsa
  • A yayin da kwamitin Agada ya ce ya gudanar da zaben fitar da gwani, kwamitin Omale ya nemi 'yan jam'iyyar da su yi watsi da zaben

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Benuwai - Da alama rikicin da ya barke a jam’iyyar APC reshen jihar Binuwai ya dauki wani salo na yadda aka gudanar da zaben fitar da gwani na jam’iyyar.

Rikicin ya sake dawowa sabo bayan da kwamitin gudanarwar jam'iyyar karkashin Benjamin Omale da na bangaren Austin Agada suka fara nunawa juna yatsa.

Kara karanta wannan

Zulum ya sake yin rashi: Kwamishinan jihar Borno ya rasu a cikin dakinsa

Sabon rikici ya sake mamaye jam'iyyar APC a jihar Benuwai
Zaben fidda gwamni ya janyo sabuwar rigima ta barke a APC reshen Benuwai.
Asali: Original

Babu zaman lafiya a jam'iyyar APC

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kwamitin SWC a karkashin jagorancin Agada, ya gudanar da zaben fitar da gwani a ranar Asabar da ta gabata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai Benjamin Omale, shugaban kwamitin rikon kwarya da aka nada, ya yi kira ga ‘yan jam’iyyar da su yi watsi da zaben da tsagin Agada ya gudanar.

Rikicin da ya barke tsakanin bangarorin biyu ya nuna yadda ake ci gaba da gwabza fada a jam’iyyar APC ta Binuwai a daidai lokacin da zaben kananan hukumomi ke gabatowa.

Asalin rikicin APC a Benuwai

Idan za a iya tunawa dai rikicin ya samo asali ne bayan da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC na kasa a Abuja ya rusa shugabancin Agada tare da nada kwamitin Omale.

A martaninsa, Agada ya bukaci babbar kotun jihar da ke Makurdi da ta ba da umarnin hana kwamitin na kasa yin katsalandan ga kwamitinsa har sai wa’adinsu ya kare.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi artabu da miyagu, an sheke 'yan bindiga a Katsina

Mai shari’a Theresa Igoche da ke jagorantar shari’ar, ta bayar da umarnin wucin gadi tare da dage sauraron karar zuwa ranar 28 ga watan Agusta, 2024.

APC: Kotu ta takawa Agada birki

A wani labarin, mun ruwaito cewa wata babbar kotun jihar Benuwai ta haramtawa Austin Agada bayyana kansa a matsayin shugaban jam'iyyar APC na jihar.

Wannan na zuwa ne yayin da shugabannin APC na gundumar Owukpa Ehaje 1, inda nan ne gundumar Agada suka dakatar da shi tare da wasu mutum shida.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.