Jigon APC Ya Juyawa Tinubu Baya, Ya Fadi Abin da Zai Sanya Ya Fadi Zaben 2027
- Jigon jam'iyyar APC a jihar Rivers, Cif Eze Chukwuemeka Eze, ya nuna cewa ƴan Najeriya ba za su zaɓi Shugaba Bola Tinubu ba a zaɓen 2027
- Na hannun daman na tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa yunwar da ake fama da ita da rashin iya za su sanya a ƙi sake zaɓar Tinubu
- Ya kuma gargaɗi masu ƙoƙarin ɓata sunan tsohon ministan a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhamadu Buhari da su shiga taitayinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Rivers - Jigon jam'iyyar APC kuma na hannun daman tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya yi magana kan yiwuwar tazarcen Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Cif Eze Chukwuemeka Eze ya bayyana cewa yunwar da ƴan Najeriya ke ciki ita za ta sanya su yi waje da Shugaba Tinubu daga kan kujerar mulkin ƙasar nan.
Jigon APC ya yi gargaɗi
Cif Eze ya kuma gargaɗi jam'iyyar APC reshen jihar Rivers ƙarƙashin jagorancin, Cif Tony Okocha da ta daina ɓata sunan tsohon gwamnan jihar Rotimi Amaechi, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Cif Eze ya gargaɗi mutanen da ke ƙoƙarin ganin sun ɓata sunan tsohon ministan da su shiga taitayinsu.
Jigon na APC ya kuma musanta iƙirarin da Tony Okocha ya yi na cewa Amaechi yana son ya yi amfani shugaban APC na Rivers, Cif Emeka Beke domin ya yaƙi Tinubu a zaɓen 2027.
Meyasa za a ƙi zaɓen Tinubu a 2027?
Cif Eze ya nuna cewa akwai tarin makaman da ƴan Najeriya suke da su waɗanda za su yi amfani da su wajen raba Shugaba Tinubu da fadar Aso Rock a zaɓen 2027.
"Rashin iya mulki, kwan gaba kwan baya kan tsare-tsare da cin hanci da rashawa waɗanda suka haɗe da rashin aikin yi, rashin tsaro, tashin farashin abinci da yunwa sune makaman da ƴan Najeriya za su yi yaƙi da su domin korar Tinubu daga ofis a 2027."
- Cif Eze Chukwuemeka Eze
Tinubu ya yi alhinin rasuwar Sarkin Ningi
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa bisa rasuwar Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya.
Shugaba Tinubu ya jajantawa al’ummar masarautar Ningi da gwamnatin jihar Bauchi bisa rasuwar marigayin wanda ya rasu a ranar Lahadi, 25 ga watan Agustan 2024.
Asali: Legit.ng