"Bai San Komai Ba": An Bukaci Tinubu Ya Sauya Ministansa cikin Gaggawa

"Bai San Komai Ba": An Bukaci Tinubu Ya Sauya Ministansa cikin Gaggawa

  • Wata kungiya ta bukaci Shugaba Bola Tinubu ya sauya Ministan man fetur, Heineken Lokpobiri saboda rashin katabus
  • Kungiyar Ijaw Youth Council ita ta bukaci Tinubu ya sauya mukamin Ministan duba da rashin aiwatar da komai a ma'aikatar
  • Matasan sun bayyana cewa Lokpobiri bai fahimci komai a harkokin man fetur ba inda suka bukaci ya sauya shi da wani dan jihar Bayelsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kungiyar Ijaw Youth Council ta bukaci Shugaba Bola Tinubu ya sauyawa Ministansa mukami a Najeriya.

Kungiyar ta shawarci Tinubu ya sauya karamin Ministan man fetur, Heineken Lokpobiri daga mukaminsa saboda rashin katabus.

Kara karanta wannan

Kama jiragen Najeriya: An bukaci DSS ta yi gaggawar kama tsohon gwamnan APC

An bukaci Tinubu ya kori Ministansa daga mukaminsa
Kungiyar matasan Ijaw ta bukaci Bola Tinubu ya sallami Heineken Lokpobiri daga mukamin Minista. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

An bukaci Tinubu ya sallami Ministansa

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kungiyar IYC ta fitar da jaridar Legit ta samu a ranar Alhamis 22 ga watan Agustan 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ta ce Lokpobiri ba shi da kwarewa game da harkokin man fetur a kasar inda ta ce sauya shi ya fi muhimmanci.

"Akwai kwararrun mutane daga jihar Bayelsa da za su iya rike mukamin fiye da Lokpobiri."
"Alamu ya nuna karara cewa Lokpobiri bai fahimci harkokin man fetur ba a kasar saboda babu wani abu da ya tsinana."

Cewar kungiyar

Kungiyar ta caccaki IYC kan Minista Lokpobiri

Sai dai wata kungiya a yankin Neja Delta ta bukaci IYC ta nemi afuwar Ministan inda ta ce hakan cin zarafi ne.

Kungiyar ta yi Allah wadai ta kalaman IYC inda ta bukace ta da ta janye kalamanta cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

"Ka da ka bata mana suna": Gwamnonin PDP sun soki Tinubu kan tallafi, sun ba da shawara

Ta ce dole IYC ta nemi yafiya daga karamin Ministan duba da yadda ake kokari a ma'aikatar da yake jagoranta a kasar.

Arewa: Tinubu ya fara shirin zaben 2027

Kun ji cewa da alamu Shugaba Bola Tinubu ya fara shirye-shiryen daukar matakai game da zaben 2027 a Arewacin Najeriya.

Ana hasashen Tinubu ya fara shirin ne da wuri domin shawo kan shugabannin Arewa da suke kushe salon mulkinsa.

Wata majiya ta bayyana irin tsare-tsaren da aka kaddamar tare da kirkirar wasu sababbi saboda shawo kan matsalolin da ke damun yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.