“PDP Ta Zama Tarihi”: Tsohon Sanatan Arewa Ya Kwancewa Jam'iyyarsa Zani a Kasuwa

“PDP Ta Zama Tarihi”: Tsohon Sanatan Arewa Ya Kwancewa Jam'iyyarsa Zani a Kasuwa

  • Tsohon dan takarar gwamnan Kogi karkashin PDP a zaben jihar na 2023, Sanata Dino Melaye ya yiwa jam'iyyarsa wankin babban bargo
  • Sanata Dino Melaye ya yi ikirarin cewa yanzu PDP ta zama tarihi yayin da shugabanninta suka wargazata tare da cefanar da ita
  • Kalaman tsohon sanatan na zuwa ne yayin da ake tunanin PDP za ta iya hukunta wasu daga shugabanninta kan zargin zagon kasa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Sabon rikici ya sake kunno kai a babbar jam'iyyar adawa kasa watau PDP yayin da tsohon sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye ya yi sabuwar fallasa.

Sanata Dino Melaye, a ranar Asabar, ya yiwa jam'iyyar ta sa wankin babban bargo inda har ya yi ikirarin cewa jam'iyyar ta zama tarihi a yanzu.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC a Arewa na shirin komawa PDP? Gwamnati ta yi magana

Sanata Dino Melaye ya yi magana kan halin da PDP ta ke ciki
Sanata Dino Melaye ya zargi shugabannin PDP da cefanar da jam'iyyar. Hoto: @_dinomelaye
Asali: Facebook

Dino Melaye ya caccaki PDP

Sanata Melaye, wanda ya yi takarar gwamnan Kogi a zaben 2023 karkashin PDP, ya fito a shafinsa na X ya yi maganganu masu daukar hankali kan halin da jam'iyyarsa ta ke ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da farko dai tsohon sanatan ya yi ikirarin cewa karshen jam'iyyar PDP ya zo yana mai cewa:

"Karshen PDP ya zo bayan da shugabannin jam'iyyar suka wargaza ta."

Sanata Melaye ya lissafa shugabannin da ya ke magana a kansu da suka hada da shugaban PDP na kasa, Iliya Damagum, da sakatarenta na kasa, Samuel Anyanwu da sataren shirye-shirye, Umar Bature.

"PDP ta zama tarihi" - Sanata Melaye

Tsohon dan majalisar dattawan ya kara da zargin cewa shugabannin da ya lissafa sun riga da sun cefanar da jam’iyyar PDP da kuma mayar da hannun 'yan kasuwa.

Kara karanta wannan

Ana zargin wasu Ƴan daba sun farmaki magoya bayan APC a harabar kotun ƙoli

“Za mu yi magana game da cefanar da jam'iyyar da suka yi. A halin yanzu PDP ta riga da ta zama tarihi."

Jaridar PDP ta rahoto cewa akwai yiwuwar kwamitin NWC na PDP zai hukunta Damagum da Anyanwu kan wata wasika da suka rubuta wa kotun daukaka kara da ke Fatakwal kan rikicin jam’iyyar.

Kogi: PDP ta ba Melaye tikiti

A wani labarin, mun ruwaito cewa wakilan zaben cikin gida na PDP a jihar Kogi, sun zabi Sanata Dino Melaye a matsayin dan takarar jam'iyyar a zaben jihar na 2023.

Sanata Dino Melaye ya samu ruwan kuri'u har 313 a zaben fidda gwamnin neman takarar kujerar gwamnan da PDP ta gudanar a dakin taro na Kafa’s Hall da ke Lokoja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.