2027: Tinubu Ya Nemo Hanyar Shawo kan Yan Arewa, an Fadi Dabarun da Ya Shirya
- Yayin da aka fara tunanin zaben 2027 tun yanzu, wasu shugabannin yankin Arewacin kasar sun fara korafi da gwamnatin APC
- Dalilin haka ne ma ya sanya Shugaba Bola Tinubu daukar wasu matakai domin shawo kan korafe-korafen daga Arewa
- Hakan bai rasa nasaba da matsalolin da yankin ke fama da su da ake ganin zai iya jawowa Bola Tinubu matsala a zaben 2027
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Da alamu Shugaba Bola Tinubu ya fara shirye-shiryen daukar matakai game da zaben 2027.
Ana hasashen Tinubu ya fara shirin ne da wuri domin shawo kan shugabannin Arewa da suke kushe salon mulkinsa.
2027: Tinubu ya fara shiri kan yan Arewa
A wani rahoto da Punch ta fitar na musamman a yau Lahadi 25 ga watan Agustan 2024, an bayyana irin shirin da shugaban ke yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata majiya ta bayyana irin tsare-tsaren da aka kaddamar tare da kirkirar wasu sababbi saboda shawo kan matsalolin.
Majiyar ta tabbatar da cewa Tinubu bai tsoron masu cece-kuce amma an dauki matakan ne domin shawo kan shugabannin yankin da ke kalubalantar zabensa a 2027.
2027: Matakai 2 da Tinubu ya dauka
"Farkon abin da za a fara yi shi ne kara mukamai a yankin Arewacin Najeriya, idan an yi haka akwai yiwuwar a rufe bakin masu korafi kan haka."
"Na biyu, shi ne dakile matsalolin rashin ilimi da talauci wanda shi ne musabbabin kirkirar hukumar Arewa maso Gabas (NEDC)."
- Cewar majiyar
Majiyar ta tabbatar da cewa an dauki wasu matakai guda biyu domin kwantar da hankula a Arewa saboda zaben 2027 da ake tunkara.
Arewa: An shawarci Tinubu kan zaben 2027
Kun ji cewa Jigon jam'iyyar PDP a Najeriya, Abdul-aziz Na'ibi Abubakar ya yi tsokaci kan zaben 2027 da 'yan Arewa.
Abdul-aziz ya ce Bola Tinubu ba zai taba samun kuri'un 'yan Arewa ba musamman bayan sanya hannu a yarjejeniyar Samoa.
Na'ibi ya ce zai yi wahala yankin Kudu maso Yammacin Najeriya su iya kawo Tinubu a zaben domin ba shi dama ta biyu.
Asali: Legit.ng