An Yada Hotunan Haduwar Ganduje, Kwankwaso da Atiku da Wasu Jiga Jigai a Abuja
- Jiga-jigan siyasar Najeriya da dama sun samu halartar daurin auren yar Atiku Abubakar a yau Juma'a a birnin Abuja
- Yayin daurin auren an gano Sanata Rabiu Kwankwaso da shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje da sauran jiga-jigan siyasar Najeriya
- An daura auren ne tsakanin Laila Abubakar da kuma Saleh Ilyasu Maitama a yau Juma'a 23 ga watan Agustan 2024
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Manyan 'yan siyasar Najeriya da dama sun samu halartar daurin auren yar Atiku Abubakar, Laila Abubakar da Saleh Ilyasu Maitama a birnin Abuja.
An daura auren ne a babban masallacin Abuja a yau Juma'a 23 ga watan Agustan 2024.
Atiku ya aurar da yarsa a Abuja
Hadimin Atiku Abubakar a bangaren sadarwa ta zamani, AbdulRasheed Shehu shi ya wallafa hotunan daurin auren a shafin X a yau Juma'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku kamar yadda hadimin nasa ya tabbatar, ya godewa duka wadanda suka samu halartar daurin auren yar tasa a Abuja.
Shehu ya ce Atiku ya yi addu'a ga ma'auratan inda ya musu fatan alheri da samun zuri'a dayyiba a rayuwar aurensu.
Aurarrakin da Ganduje ya halarta a Abuja
Bayan halartar auren diyar Atiku, Ganduje ya kuma halarci daurin auren dan tsohon Ministan Iimi, Adamu Adamu.
Adamu Adamu shi ne tsohon Ministan Ilimi a mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari daga 2015 zuwa 2023.
Tsohon hadimin shugaban APC, Salihu Tanko Yakasai shi ya wallafa hotunan Ganduje yayin haartar daurin auren a yau Juma'a 23 ga watan Agustan 2024.
Atiku ya zargi Tinubu da lalata kasa
Kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya zargi shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da kokarin lalata kasar nan.
Haka kuma Atiku Abubakar na ganin iyalan shugaba Tinubu da abokansa na kokarin cefanar da kasar nan gabanin kammala wa'adinsa.
Tsohon shugaban kasar Najeriya ya yi zargin cewa a halin da ake tafiyar da kasar nan a yanzu sai an sha wahala kafin a gyara barnar da tafka a baya.
Asali: Legit.ng