Bidiyon Matasa Sun Farmaki Dan Takarar Gwamna Bayan Hukunci a Kotun Koli

Bidiyon Matasa Sun Farmaki Dan Takarar Gwamna Bayan Hukunci a Kotun Koli

  • Matasa sun farmaki dan takarar gwamna a jam'iyyar SDP, Murtala Ajaka bayan hukuncin Kotun Koli a birnin Abuja
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa ana zargin matasan 'yan APC ne da ke goyon bayan Gwamna Usman Ododo na jihar Kogi
  • Wannan na zuwa ne mintuna kadan bayan Kotun Koli ta yi fatali da korafin Ajaka a zaben da aka gudanar a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Jim kadan bayan yanke hukunci a Kotun Koli, yan daba sun farmaki dan takarar gwamna a jihar Kogi.

Matasan sun kai farmaki kan dan takarar a jam'iyyar SDP, Murtala Ajaka duk da rashin nasara da ya yi a Kotun Koli.

Kara karanta wannan

Zaben kananan hukumomi: APC ta ba dan acaba tikitin tsayawa takara a Arewa

Matasa sun farmaki dan takarar gwamna bayan hukuncin Kotun Koli
Wasu yan daba sun kai hari kan dan takarar gwamna a Kogi, Murtala Ajaka. Hoto: @AlhMuriAjaka, @OfficialOAU.
Asali: Twitter

Kogi: Yadda aka farmaki dan takarar gwamna

A cikin wani faifan bidiyon da TVC News ta wallafa, an gano yadda matasan m suka zagaye Ajaka a farfajiyar kotun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'an tsaro sun ba da gudunmawa wurin kare Ajaka yayin da matasan ke kokarin masa illa bayan hukuncin.

An gano yadda jami'an tsaro suka kange shi domin ba shi kariya har zuwa cikin motarsa inda ya zura a guje.

Matasan sun yi ta dukan motar lokacin da ya shiga cikinta duk da jami'an tsaron da ke wurin.

Hukuncin kotu kan shari'ar zaben gwamnan Kogi

Wannan na zuwa ne jim kaɗan bayan Kotun Koli ta raba gardama kan shari'ar zaben gwamnan Kogi.

Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Usman Ododo na APC kamar yadda hukumar zabe ta INEC ta tabbatar.

Har ila yau, kotun ta yi fatali da korafe-korafen yan takarar jam'iyyun SDP da kuma AA a zaben saboda rashin gamsassun hujjoji.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun cafke rikakkun na hannun daman Bello Turji a wani bidiyo

Kotu ta yi hukunci a zaben Bayelsa

A wani labarin, kun ji cewa Kotun Koli ta raba gardama kan shari'ar zaben gwamnan jihar Bayelsa.

Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Douye Diri na jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan.

Har ila yau, kotun ta yi fatali da korafe-korafen dan takarar gwamnan Bayelsa a jam'iyyar APC, Mr. Timipre Sylva.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.