Rikicin PDP: An ba Ministan Tinubu Mafita kan Takaddamarsa da Jam'iyyar Adawa
- Ministan harkokin babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike na ci gaba da shan suka kan zaman yake yi a jam'iyyar adawa ta PDP
- Tsohon mai ba PDP shawara kan harkokin shari'a ya buƙaci tsohon gwamnnan na jihar Rivers da ya tattara kayansa ya fice daga jam'iyyar
- Mark Jacob ya zargi Wike da ruruta rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam'iyyar PDP inda ta ƙara da cewa ministan na tsoron barin PDP
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon mai ba jam'iyyar PDP shawara kan harkokin shari'a, Mark Jacob, ya ba Nyesom Wike shawara.
Mark Jacob ya buƙaci ministan na birnin tarayya Abuja, da ya mutunta kansa ta hanyar ficewa daga jam'iyyar PDP.
Mark Jacob ya ba Wike wannan shawarar ne a wata hira da aka yi da shi a tashar Arise News a shirinsu na ‘Morning Show’ ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane zargi aka yiwa Wike a rikicin PDP?
Jaridar Premium Times wacce ta bibiyar tattaunawar ta ce ya zargi Wike wanda minista ne a gwamnatin Bola Tinubu, da ruruta wutar rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam'iyyar PDP.
Mark Jacob ya nuna cewa ministan ko kaɗan ba shi da dattako saboda abubuwan da yake yi.
"Ina yi masa kallon matsoraci wanda ba zai iya barin PDP ya koma APC ba. Tun da har yana adawa da PDP, idan yana son a mutunta shi ya kamata ya yi murabus daga PDP."
"Bai kamata ka zama baki biyu ba a lokaci ɗaya. Bai yiwuwa kana adawa da PDP sannan kana cewa har yanzu kana cikin PDP."
"Lokaci ya yi da za a gaya masa gaskiya. Bai yiwuwa kana cewa kai ɗan PDP ne sannan kana faɗa da ita, babu a inda ake yin haka."
- Mark Jacob
Wike ya magantu kan sulhu da Fubara
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan rikicinsa da Gwamna Siminalayi Fubara
Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya yi watsi da yiwuwar sasantawa tsakaninsa da Gwamna Fubara wanda ya gaje shi wajen rike madafun ikon jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng