Rikici Ya Dawo Ɗanye, An Fara Shirin Waje da Gwamnan Jam'iyyar PDP a Najeriya
- Ga dukkan alamu babu ranar sasanta rikicin siyasar jihar Ribas yayin da ƴan NWC PDP suka fara haɗa kai da ministan Abuja, Nyesom Wike
- Rahotanni sun nuna rikicin ya raba kawunan shugabannin PDP na ƙasa, tsagi ɗaya na tare da Wike yayin da sauran ke goyon bayan Fubara
- Kwamitin gudanarwa na PDP ta ƙasa (NWC) ya gudanar da taro kwanan nan domin tattauna halin da jam'iyyar ke ciki a jihar Ribas
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers - Wasu daga cikin mambobin kwamitin gudanarwa (NWC) na PDP ta ƙasa sun fara haɗa kai da ministan Abuja, Nyesom Wike domin tsige gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara.
Wannan dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan kwamitin amintattun PDP sun kaiwa Gwamna Fubara ziyara, inda suka ce ba za su bari Ribas su suɓuce masu ba.
A rahoton da Punch ta tattara ranar Alhamis, 22 ga watan Agusta, 2024, rikicin siyasar da ke faruwa a Ribas ya raba kawunan shugabannin PDP na ƙasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rivers: An sabunta shirin tsige Fubara
Wani babban ƙusa a NWC ya bayyana cewa akalla shugabanni 12 na PDP na bin umarnin Nyesom Wike wajen takun saƙa da Gwamna Fubara.
Wadanda ake zargin suna da hannu a shirin sauke Gwamna Fubara sun haɗa da sakataren PDP na ƙasa, Samuel Anyanwu da sakataren tsare-tsare, Umar Bature.
Mataimakin sakataren PDP na ƙasa, Setonji Koshoedo da wasu mambobin NWC takwas na cikin waɗanda suka koma tsagin Wike a rigimar siyasar Ribas.
Mambobi NWC 3 na tare da Fubara
Duk da wannan shiri da suke yi, mutum uku daga cikin mambobin NWC da suka haɗa da mai ba da shawara kan harkokin shari'a, Debo Ologunagba, sun ce suna goyon bayan Fubara.
Kazalika wata majiya daga NWC PDP ta ƙara da cewa a halin yanzu jam'iyyar reshen jihar Ribas za ta ci gaba da gudanar da harkokinta ƙarƙashin Wike, Leadership ta kawo.
Gwamna Fubara ya musanta barin PDP
Ku na da labarin Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya tabbatar da cewa yana nan daram a matsayin ɗan jam'iyyar PDP kuma ba shi da shirin sauya sheka.
Fubara ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi bakuncin tawagar kwamitin amintattun PDP karkashin jagorancin Adolphus Wabara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng