Wike Ya Yi Maganar Yiwuwar Sasantawa kan Rikicinsa da Gwamna Fubara

Wike Ya Yi Maganar Yiwuwar Sasantawa kan Rikicinsa da Gwamna Fubara

  • Ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa babu batun sasantawa tsakaninsa da gwamnan jihar Rivers
  • Wike ya ce yanzu ya maida hankalinsa wajen sauke nauyin da Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ɗora masa a birnin tarayya Abuja
  • Ya yi nuni da cewa Gwamna Siminalayi Fubara ne ya nuna baya son su kasance tare saboda haka kowa ya yi ta kansa a siyasance

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan rikicinsa da Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers.

Wike ya yi watsi da yiwuwar sasantawa tsakaninsa da gwamnan wanda ya gaje shi wajen rike madafun ikon jihar.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya faɗi gaskiya kan jita jitar yana shirin sauya sheƙa

Wike ya yi magana kan rikicinsa da Fubara
Wike ya ce ba zai sasanta da Gwamna Fubara ba Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS, Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Wike ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai domin cikarsa shekara ɗaya a ofis a matsayin ministan babban birnin tarayya Abuja a ranar Laraba, cewar rahoton jaridar PM News.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shin Wike zai sasanta da Gwamna Fubara?

Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya ce ba zai ja da baya ba kan shawarar da ya yanke kan Gwamna Fubara.

Wike ya ce yanzu mayar da hankali ne wajen sauke nauyin da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ɗora masa ba goyon bayan Gwamna Fubara ba, rahoton Daily Post ya tabbatar da haka.

"Na yi yaƙi domin Fubara ya zama gwamna ba tare da wata nadama ba, amma yanzu ya ce ba ya son ya kasance tare da mu, babu matsala. Tinubu ne ya kawo Aregbesola amma yanzu ba su tare da shugaban ƙasa."
"Magana ta gaskiya ita ce babu batun ja da baya kuma mutane na sun sani. Wane goyon baya? Wasu mutanen ba su yin siyasa mai nagarta, amma ni ina yi. Shi ne ya ce kowa ya yi ta kansa saboda haka a bari na yi ta kaina."

Kara karanta wannan

Bayan nasara a kotu, mataimakin gwamna ya ba gwamnan PDP shawara

"Hakan bai dame ni ba saboda na mayar da hankalina kan aikin da shugaban ƙasa ya ba ni a birnin tarayya Abuja."

- Nyesom Wike

Wike ya magantu kan ficewa daga PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, a ranar Laraba, 21 ga watan Agusta, ya sha alwashin ci gaba da zama a jam’iyyar PDP.

Ministan ya kuma musanta jita-jitar da ake yaɗawa cewa yana shirye-shiryen sauya sheƙa daga PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng