Kwankwaso Ya Samu Goyon Baya, An Faɗi Wanda Ya Dace da Mulkin Najeriya a 2027
- Yayin da ake tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na gaba a 2027, Rabiu Kwankwaso ya fara samun cikakken goyon baya a NNPP
- Shugaban ƙungiyar ciyamomin NNPP a jihohi, Tosin Adeyemi, ya ce lokaci ya yi da ƴan Najeriya za su zaɓi nagartaccen shugaba
- Ya ce Kwankwaso mutum ne mai kishin ƙasa kuma burinsa ya gina Najeriya yadda kowane ɗan ƙasa zai alfahari da ita
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Osun- Shugaban ƙungiyar ciyamomin jam'iyyar NNPP na jihohi, Tosin Odeyemi, ya buƙaci ƴan Najeriya su shure addini da ƙabila wajen zaɓen shugabannni a zaɓen 2027.
Mista Odeyemi, wanda shi ne shugaban NNPP na jihar Osun ya ce tun yanzu ya kamata ƴan Najeriya su fara shirye-shiryen zaɓe na gaba domin da safe-safe ake kama fara.
Ya ce lokaci ya yi da mutane za su tsaya kai da fata, su tabbatar sun zaɓi nagartaccen shugaba wanda zai share masu hawaye, Premium Times ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wata sanarwa da ya fitar a Osun, Odeyemi ya ce a bayyane yake PDP da APC sun gaza ceto ƴan Najeriya daga matsaloli kamar talauci, cin hanci da rashin tsaro.
2027: Kwankwaso ya samu goyon baya
Yayin da yake nuna goyon baya ga jagoran NNPP Rabiu Kwankwaso, Tosin Adeyemi ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su su kaucewa son zuciya, su zabi wanda ya dace da mulkin Najeriya.
A rahoton Vanguard, Adeyemi ya ce:
"Kishin Kwankwaso na ganin Najeriya ta gyaru ta kai matakin da kowane dan kasa na gida da waje zai yi alfahari da ita, shi ne ya sa mutane da dama ke ƙaunarsa.
"Babban burin da ya sa a gaba tun 2018 shine ya zama shugaban Najeriya wanda zai jagoranci sabuwar kasa kuma zai fi ba da fifiko kan ilimi da ci gaban tattalin arziki.
"Tun da ya shigo NNPP, jam'iyyar ta sauya, yanzu tana da gwamna, sanatoci, ƴan majalisar wakilai, ƴan majalisar jiha, ciyamomi da kansiloli."
Odeyemi ya bukaci a zaɓi Kwankwaso
Yayin da ake tunkarar zaben shugaban kasa a 2027, Mista Odeyemi ya bayyana cewa Najeriya na bukatar mutun mai daraja kamar Kwankwaso.
Wani jigon NNPP a Kano, Malam Saidu Abdullahi ya shaidawa Legit Hausa cewa tabbas lokaci ya yi da ƴan Najeriya za su natsu su zaɓi shugabanni na gari.
Ya ce a ganinsa ba sai an tsaya ɓata lokacin yiwa mutane bayanin wanda ya dace su zaɓa ba, a yanzu kowa yana ji a jikinsa.
Jigon ya ce:
"Tun kafin zaɓen 2023 muke gayawa mutane kada su sake zaɓen APC, mutanen nan sun yi shekara takwas babu uwar da suka tsinana, to yanzu dai kowa na ji a jiki.
"Idan Allah ya kaimu 2027, mu dai muna nan a inda aka san mu tun asali, Kwankwaso kawai, shi ne mutum ɗaya mai kishin da babu kamarsa a Arewa."
Sauya tambarin NNPP ya bar baya da ƙura
A wani rahoton kuma yayin da Rabi'u Kwankwaso ya sauya tambarin NNPP, ya gamu da cikas daga wanda ya kirkiro jam'iyyar adawar a Najeriya.
Dakta Boniface Aniebonam ya caccaki Kwankwaso da hukumar INEC kan sauya tambarin da kuma launin jam'iyyar gaba daya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng