Cikin Jam'iyyar APC Ya Ɗuri Ruwa Bayan Kiran Jonathan Ya Tsaya Takara a 2027

Cikin Jam'iyyar APC Ya Ɗuri Ruwa Bayan Kiran Jonathan Ya Tsaya Takara a 2027

  • Kiraye-kiraye sun fara yin nisa kan tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya dawo karasa wa'adi na biyu a Aso Rock
  • Ko a kwanaki an jiyo gwamnan Bauchi, Bala Muhammad na ikirarin zai fasa neman takara matukar Jonathan zai dawo
  • A martanin APC, PDP ta yi garaje domin ya yi wuri ta fara maganar 2027, duk da haka jam'iyyar na ganin Jonathan zai fadi zabe

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Ana ta samun karuwar kiraye-kiraye daga ciki da wajen jam'iyyar PDP na ganin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya sake neman takara.

Wasu daga cikin kusoshin jam'iyyar kamar Gwamnan Bauchi, Bala Muhammad ya bayyana cewa za su marawa Jonathan baya matukar ya amince ya tsaya a 2027.

Kara karanta wannan

Shugaban NLC, Ajaero ya yi fatali da gayyatar yan sanda, ya mika bukatunsa

Bola Tinubu
PDP ta fara shirin tsayar da Jonathan takarar 2027 Hoto: Goodluck Jonathan/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa da ya ke martani, sakataren yada labaran PDP, Ibrahim Abdullahi ya ce ra'ayin gwamna Bala ya zo dai-dai da na dattawan jam'iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kan batun Atiku, jam'iyyar PDP na ganin lokaci ya zo da tsohon mataimakin shugaban kasar zai hakura ya marawa wanda jama'a za su so baya.

APC na tsoron takarar Jonathan PDP?

Tuni jam'iyyar APC ta yi martani kan kokarin sake tsayar da Goodluck Jonathan takarar shugaban kasa, inda ta ke ganin ya yi wuri a fara wannan zancen.

Daraktan yada labaran APC na kasa, Bala Ibrahim ya ce kame-kame kawai PDP ke yi, kuma ba zai haifar mata da da mai ido ba a kakar zaben 2027.

Bala Ibrahim ya jaddada cewa kokarin tsayar da Jonathan ba zai girgiza su ba, domin su na da tabbacin jama'a za su sake zabar Bola Tinubu a karo na biyu.

Kara karanta wannan

NLC ta ja daga, ta fadi tsattsauran mataki idan aka kama shugabanta, Ajaero

Matasa sun fara marawa PDP baya

A baya mun ruwaito cewa wasu matasan kasar nan sun fara daura damarar takarar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar don zaben 2027.

Kungiyar ta Nigeria Youths for Atiku (NYA) ta bayyana cewa babu wani mahaluki da zai hana Atiku Abubakar tsayawa takara da samun nasara a zaben.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.