Bayan Nasara a Kotu, Mataimakin Gwamna Ya Ba Gwamnan PDP Shawara

Bayan Nasara a Kotu, Mataimakin Gwamna Ya Ba Gwamnan PDP Shawara

  • Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, ya ba Gwamna Godwin Obaseki shawara kan hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke
  • Philip Shaibu ya buƙaci gwamnan da ya mutunta hukuncin kotun wanda ya tabbatar da shi a matsayin mataimakin gwamnan jihar
  • Mataimakin gwamnan ya bayyana cewa Gwamna Obaseki ya saba sanya ƙafa ya shure hukuncin kotu ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu ya yi kira da babbar murya ga Gwamna Godwin Obaseki na jihar.

Philip Shaibu ya buƙaci gwamnan da ya ya yi biyayya ga hukuncin da kotun ɗaukaka kara da ke Abuja ta yanke a ranar Talata maimakon ya wuce zuwa Kotun Ƙoli.

Kara karanta wannan

Wike ya yi maganar yiwuwar sasantawa kan rikicinsa da Gwamna Fubara

Philip Shaibu ya shawarci Gwamna Obaseki
Philip Shaibu ya bukaci Gwamna Obaseki ya mutunta hukuncin kotu Hoto: Comrade Philip Shaibu, Governor Godwin Obaseki
Asali: UGC

Philip Shaibu, a wata sanarwa da babban sakataren yada labaransa, Ebomhiana Musa, ya fitar, ya bayyana cewa ana buƙatar zaman lafiya domin ciyar da jihar Edo gaba, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun ɗaukaka ƙarar ta tabbatar da Philip Shaibu a matsayin halastaccen mataimakin gwamnan jihar.

Wace shawara Shaibu ya ba Gwamna Obaseki?

"Wannan wata nasara ce ga dimokuraɗiyya da bin doka da oda. Muna fatan Obaseki zai yi biyayya ga wannan sabon hukunci na kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja.
"Obaseki ba ya mutunta hukunce-hukuncen kotu. Shi yana ɗaukar kansa a matsayin doka."
"A bisa wannan hukuncin da kotu ta yi, muna sa ran Obaseki zai ajiye girman kansa, ya manta da komai sannan ya gayyaci Shaibu domin tattaunawa mai ma'ana, saboda amfanin mutanen jihar Edo."

- Ebomhiana Musa

Sakataren yaɗa labaran ya kuma bayyana mulki a matsayin abu na wucin gadi, inda ya nanata cewa a ranar 12 ga watan Nuwamba, wani ne zai zama gwamnan Edo yayin da Obaseki zai zama tsohon gwamna.

Kara karanta wannan

Gwamnan Plateau ya dakatar da manyan jami'an gwamnati mutum 4

Philip Shaibu ya fice daga PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu ya sanar da ficewa daga jam'iyyar PDP a mai mulki a jihar.

Philip Shaibu wanda babbar kotun tarayya ta dawo da shi kan muƙaminsa bayan tsige shi da majalisar dokokin jihar ta yi ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng