Zaben Kano: NNPP Ta Tanadin Katin WAEC da NECO, Za a Duba Takardun Karatun Yan Takara

Zaben Kano: NNPP Ta Tanadin Katin WAEC da NECO, Za a Duba Takardun Karatun Yan Takara

  • Jam'iyyar NNPP da ke mulki a Kano ta fara shirin tsayawa takarar shugabanci a kananan hukumomi 44 a fadin jihar
  • A makon da ya gabata ne hukumar shirya zabe mai zaman kanta (KANSIEC) ta ce za a gudanar da zabukan a watan Nuwamba
  • NNPP ta fara kokarin tabbatar da sahihancin karatun kammala sakandaren masu son tsayawa takarar da za a shiga

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Jam'iyya mai mulki a Kano, NNPC ta sayawa kwamitin tantance yan takara karamar hukuma katin duba jarrabawar kammala sakandare ta WAEC da NECO.

Wannan na zuwa ne a wani yunkuri na tabbatar da sahihancin shaidar kammala sakandaren 'yan takararta gabanin ranar 30 Nuwamba, 2024 da za a yi zaben.

Kara karanta wannan

NNPP ta yanke kudin tsayawa takara a zaben kananan hukumomin Kano

Abba Kabir
NNPP za ta binciki yan takararta a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa shugaban NNPP a Kano, Hashim Dungurawa ne ya shaidawa manema labarai hakan ranar Talata a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hon. Dungurawa ya ce an sanya kudin tsayawa takarar shugaban karamar hukuma a kan N500,000, sai N100,000 domin bayyana sha'awar tsayawa takarar.

Jam'iyyar NNPP za ta yi gwajin kwaya

Jam'iyyar NNPP ta bayyana cewa za ta binciki dukkannin yan takararta da ke shirin tsayawa takara a zaben kananan hukumomi mai zuwa, Independent News ta tattaro.

Shugaban jam'iyyar, Hashim Dungurawa ne ya bayyana haka ga manema labarai, inda ya ce za su sayar da takardar tsayawa takarar Kansila a kan N150,000.

Za a kuma a biya N50,000 domin bayyana sha'awar tsayawa takarar, inda Hon. Dungurawa ya ce sun yi ragin ne saboda halin matsi da gwamnatin Tinubu ta jefa jama'a.

Kara karanta wannan

NLC ta ja daga, ta fadi tsattsauran mataki idan aka kama shugabanta, Ajaero

NNPP ta yanke kudin tsayawa takara

A wani labarin kun ji cewa jam'iyyar NNPP a Kano ta yanke kudin tsayawa takarar shugabancin mukamai daban-daban a zaben kananan hukumomi da za a yi a Nuwamba.

Shugaban Jam'iyyar na jiha, Hashim Dungurawa ya bayyana cewa masu son tsayawa takarar shugaban karamar hukuma za su biya N600,000, kansiloli kuma N200,000.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.