NNPP Ta Yanke Kudin Tsayawa Takara a Zaben Kananan Hukumomin Kano

NNPP Ta Yanke Kudin Tsayawa Takara a Zaben Kananan Hukumomin Kano

  • Jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano ta sanar da kuɗaden siyan fom ga masu shawarar tsayawa takara a zaɓen ƙananan hukumomin jihar
  • Shugaban jam'iyyar na jihar, Hashimu Dungurawa, ya ce masu son yin takarar Ciyaman za su biya N600,000 sannan Kansiloli su biya N200,000
  • Shugaban na NNPP ya buƙaci masu riƙe da muƙamai da ke son yin takara da su tabbatar sun yi murabus kamar yadda dokar kasa ta tanada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Jam’iyyar NNPP a Kano ta yanke kuɗaɗen siyan fom ga masu shawarar tsayawa takara a zaɓen ƙananan hukumomin jihar.

Jam'iyyar ta sanya N500,000 a matsayin kuɗin fom ɗin takarar shugaban ƙaramar hukuma, sai N150,000 na takarar Kansila. Sai kuɗin na gani ina so N100,000 da N50,000.

Kara karanta wannan

Zaben Kano: NNPP ta tanadin katin WAEC da NECO, za a duba takardun karatun yan takara

NNPP ta yanke kudin fom a Kano
NNPP ta yanke kudin fom domin takara a zaben kananan hukumomin Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Jam'iyyar NNPP ta yanke kuɗin fom a Kano

Shugaban jam’iyyar NNPP na Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Talata, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma bayyana aniyar jam’iyyar na ba dukkanin masu son tsayawa takara a zaben ƙananan hukumomi da ke tafe dama domin su gwada sa'arsu.

Hashimu Dungurawa ya yi kira ga masu sha’awar tsayawa takara waɗanda ke riƙe muƙamai da su yi murabus kamar yadda hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano (KANSIEC) ta tanada.

NNPP ta yabi hukumar KANSIEC

Shugaban NNPP ya ƙara da cewa kuɗin sha'awar tsayawa takara na N10m ga masu son takarar shugaban ƙaramar hukuma da N5m ga masu son takarar Kansila da hukumar KANSIEC ta sanya abin a yaba ne.

Ya bayyana cewa sanya kuɗin zai sanya mutane masu nagarta da hankali ne kaɗai za su shiga takara a zaɓen.

Kara karanta wannan

Ganduje ya yi maganar neman takarar shugaban ƙasa a 2027, ya zargi ƴan Kwankwasiyya

Ɗan takarar NNPP ya lashe zaɓe

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar jam'iyyar NNPP ya samu nasarar lashe kujerar Kansila a zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar a jihar Adamawa.

Jam'iyyar PDP ta lashe duka mazaɓu guda 226 inda jam'iyyar NNPP kuma ta yi nasara a kujerar Kansila a mazaɓar Demsa a ƙaramar hukumar Demsa da ke jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng