Jam’iyyun Adawa Sun Hada Kai, Sun Ragargaje Tinubu kan Sayen Sabon Jirgi

Jam’iyyun Adawa Sun Hada Kai, Sun Ragargaje Tinubu kan Sayen Sabon Jirgi

  • Masana da yan kasa na cigaba da fashin baki kan sayen sabon jirgin da fadar shugaban kasa ta yi ga shugaba Bola Ahmed Tinubu
  • Yan siyasa sun caccaki gwamnatin tarayya kan sayen sabon jirgin a daidai lokacin da Najeriya ke fama da matsalar tattali
  • A ranar Litinin ne shugaba kasa Bola Tinubu ya fara hawan sabon jirgin shugaban kasa da aka saya masa zuwa kasar waje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na cigaba da shan suka kan sayen sabon jirgin shugaban kasa.

An bayyana matakin da gwamnati ta dauka na sayen jirgin a matsayin kuskure lura da halin da kasa ke ciki.

Kara karanta wannan

Airbus A330: Abin da ya kamata ku sani game da sabon jirgin shugaban kasar Najeriya

Jirgin Tinubu
An soki Tinubu kan sayen sabon jirgi. Hoto: Ajuri Ngalele
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito yadda yan jam'iyyun adawa da dama suka soki gwamantin tarayya kan sayen jirgin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

LP: 'Tinubu ya fifita kansa'

Kakakin dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Yunusa Tanko ya caccaki Tinubu kan sayen jirgin inda ya ce bai damu da matsalolin Najeriya ba.

Yunusa Tanko ya ce yadda shugaban kasa ya saye jirgi a wannan lokaci ya nuna cewa ba damuwar yan kasa ba ce a gabansa.

Osadolor: 'Tinubu ya karya doka'

Shugaban matasan jam'iyyar PDP, Timothy Osadolor ya ce kwata kwata lamarin sayen jirgin ya sabawa doka.

Timothy Osadolor ya kara da cewa gwamnati ta nuna rashin tausayi kan yadda ta saye jirgin shugaban kasa a lokacin da ake shan wahala a Najeriya.

Jirgin Tinubu: Sowore ya yi martani

Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore ya wallafa a Facebook cewa akwai rashin tausayi wajen sayen jirgin.

Kara karanta wannan

Rashawa: Kashim Shettima ya fadi hanyar da Tinubu ya kamo domin cafke barayi

Omoyele Sowore ya ce Bola Tinubu ya koka kan cewa shekara daya ta yi kadan ya canza abubuwa amma a shekara daya ya saye sabon jirgi.

Gwamnati ta yi bayani kan tallafin mai

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta yi karin haske kan maganar da Bola Tinubu ya yi ga kamfanin NNPCL na cigaba da biyan kudin tallafin man fetur.

Shugaban harkar tattara kudi na kamfanin NNPCL, Alhaji Umar Ajiya ne ya yi bayanin ga yan Najeriya bayan al'umma sun shiga ruɗani.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng