Matashi dan Shekara 28 Ya Lashe Zaben Ciyaman a Bauchi, Ya Rantsar da Kansiloli 17

Matashi dan Shekara 28 Ya Lashe Zaben Ciyaman a Bauchi, Ya Rantsar da Kansiloli 17

  • Dan shekara 28, Pharm. Ibrahim Abubakar Dembo ya samu nasarar lashe zaben ciyaman a karamar hukumar Toro, jihar Bauchi
  • Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya rantsar da Pharm Ibrahim tare da sauran 'yan takara 19 da suka ci zaben kananan hukumomin
  • An ruwaito cewa sabon shugaban ya kasance matashi mai hazaka da nutsuwa, wanda ya taba rike mukamin hadimi ga Gwamna Bala

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Bauchi - Gwamnan Bala Mohammed ya rantsar da shugabannin kananan hukumomi 20 na jiharsa ta Bauchi bayan samun nasara a zaben da aka kammala.

Daga cikin ciyamomin da gwamnan ya rantsar, akwai Pharm. Ibrahim Abubakar Dembo, wani matashi dan shekara 28 da ya ci zabe a karamar hukumar Toro.

Kara karanta wannan

Zaben Kano: NNPP ta tanadin katin WAEC da NECO, za a duba takardun karatun yan takara

Dan shekara 28 ya lashe zaben shugaban karamar hukuma a Bauchi
Gwamnan Bauchi ya rantsar da dan shekara 28 matsayin shugaban karamar hukuma. Hoto: Buhari A Toro
Asali: Facebook

Buhari A Toro, wani dan karamar hukumar Pharm. Ibrahim ne ya fitar da rahoton rantsar da sabon shugabansu a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Samun nasarar matashi Ibrahim a zaben kananan hukumomin jihar ya kara karsashi a zukatan matasa masu niyyar shiga harkar siyasa.

Dan shekara 28 ya zama ciyaman a Bauchi

Buhari Toro ya wallafa cewa:

"Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya rantsar da Pharm. Ibrahim Abubakar Dembo tare da sauran takwarorinsa 20 na jihar.
"Bayan rantsar da shi, mai girma ciyaman shi ma ya rantsar da kansilolin karamar hukumarsa ta Toro su 17 a sakatariyar karamar hukumar.
"Wadanda suka halarci bikin rantsar da kansilolin sun hada da shugaban jam'iyyar PDP na karamar hukumar Toro Alh. Usama Wundi da sauran tawagarsa."

Duba sanarwar a kasa:

Dan makarantarsu Ibrahim ya magantu

Kara karanta wannan

Jihar Kudu ta nemi daukin shugaban APC Ganduje domin ceto siyasar Tinubu a 2027

Muhd El-Bonga Ibraheem, wanda ya bayyana kansa a matsayin yayan sabon ciyaman din Toro lokacin suna makarantar sakandare, ya magantu a shafinsa na Facebook.

Muhd Ibraheem ya ce:

"Ibrahim yana da hankali da nutsuwa. Ya kasance daya daga cikin zakakuran dalibai a lokacin yana makarantar sakandare ta Gwagwalada, Abuja, inda muka yi karatu tare.
"An fara nada Ibrahim a matsayin mataimaki na musamman ga Gwamna Bala Muhammad lokacin da ya ci zabe a 2019.
"Ya kasance babban masoyin Bala Muhammad tun daga lokacin da yake sanata, minista har zuwa yanzu da ya ke gwamna. Jajurcewa da biyayya ta yi rana."

Duba bayanin El-Bonga a kasa:

Dan takarar PDP ya sha kasa a Bauchi

A wani labarin, mun ruwaito cewa dan takarar AAC ya kayar da takwaransa na PDP a zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar a jihar Bauchi.

Hukumar zaɓe ta BSIEC, ta sanar da Yunusa Muhammad na AAC a matsayin wanda ya lashe kujerar kansila ta mazabar Papa a karamar hukumar Darazo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.