APC Vs SDP: Kotun Koli Ta Shirya Yanke Hukunci a Shari'ar Neman Tsige Gwamnan Kogi

APC Vs SDP: Kotun Koli Ta Shirya Yanke Hukunci a Shari'ar Neman Tsige Gwamnan Kogi

  • Kotun Koli ta tanadi hukunci a karar da Murtala Ajaka dan takarar SDP ya shigar na kalubalantar nasarar Usman Ododo a zaben Kogi
  • Ajaka ya daukaka kara kan hukuncin dakotun zabe ta yi na tabbatar da zaben Ahmed Usman Ododo na APC a matsayin gwamnan Kogi
  • Sai dai bayan hukuncin kotun daukaka kara a watan Yuni, Ajaka ya garzaya Kotun Koli yana mai cewa akwai kura-kurai a hukuncin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A yau Litinin, 19 ga watan Agustan 2024, Kotun Koli ta tanadi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Kogi da ke Arewacin Najeriya.

Jam'iyyar SDP da dan takararta, Murtala Ajaka ne suka shigar da kara a Kotun Kolin, inda suke neman a tsige Gwamna Ahmed Usman Ododo na APC.

Kara karanta wannan

PDP v APC: Kotun Koli ta shirya yin hukunci a shari'ar zaben gwamna

Kotun Koli ta tanadi hukunci kan zaben gwamnan jihar Kogi
Kotun Koli ta jingine hukunci kan shari'ar zaben gwamnan Kogi. Hoto: @OfficialOAU
Asali: Twitter

SDP ta samu matsala a Kotun Koli

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Kotun Koli ta jingine hukunci kan shari'ar, wadda SDP ke ƙalubalantar hukuncin kotun zabe da ta daukaka kara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun da fari, lauyan Mista Ajaka ya nemi kotun da ta amince a kafa kwamitin da zai saurari karar da suka shigar, rokon da kotun ta ki karba.

A zaman kotun na Litinin, Pius Akubo, SAN, ya shaidawa kotun cewa ya shigar da bukata ga shugaban alkalan Najeriya da ya amince Kotun Kolin ta saurari karar da suka daukaka.

Mista Akubo ya nemi da a kara yawan alkalan Kotun Kolin daga biyar zuwa bakwai domin sauraron shari'arsu.

Kotun Koli ta shirya hukuncin zaben Kogi

Bayan sauraron bangarorin biyu, Mai shari'a Garba Lawal da ke jagorantar alkalan kotun biyar ya yanke hukuncin cewa babu bukatar ƙarin alkalai a shari'ar.

Kara karanta wannan

Rahoto: Kotun Koli ta fara zaman karshe kan shari'ar zaben gwamnan Kogi da Bayelsa

Kotun Koli ta jingine yanke hukunci kan shari'ar inda ta shaidawa bangarorin biyu cewa za ta tuntube su domin sanar da su ranar yanke hukuncin karshe.

Wannan na zuwa bayan lauyan APC ya nemi kotun ta kori karar da SDP ta shigar saboda rashin cancanta da madogara, inji rahoton Leadership.

Kogi: Kotun daukaka kara ta yi hukunci

Tun da fari, mun ruwaito cewa Kotun Daukaka Kara da ke da zama a Abuja ta tabbatar da zaben Usman Ododo a matsayin gwamnan jihar Kogi.

Kotun mai alƙalai uku ta yanke hukuncin yin watsi da ƙarar jam’iyyar SDP da ɗan takararta na gwamna, Murtala Ajaka suka shigar yana mai rokon a soke nasarar Ododo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.