Rahoto: Kotun Koli Ta Fara Zaman Karshe Kan Shari'ar Zaben Gwamnan Kogi da Bayelsa
Abuja – Kotun Koli ta fara zaman karshe kan rigingimun da suka kunno kai bayan kammala zaben wasu jihohi da ba a yi su tare da babban zaben 2023 ba.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kamar yadda rahotanni suka bayyana a ranar Litinin, 19 ga watan Agusta, 2024, zaman kotun ya shafi kararrakin zaben zaben jihohin Kogi da Bayelsa a watan Nuwamba 2023.
Rahoton Channels TV ya nuna cewa hukumar INEC ta bayyana Usman Ododo ne ya lashe zaben gwamnan Kogi, sai kuma Duoye Diri ya yi nasara a Bayelsa.
Legit Hausa ta ruwaito Gwamna Ododo ya yi nasara a karkashin jam'iyyar APC ne yayin da Gwamna Diri ya ci zabe a karkashin jam'iyyar PDP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A Kogi, Muritala Ajaka na jam’iyyar SDP na kalubalantar sanarwar da INEC ta yi kan sakamakon zaben jihar.
Hakazalika, tsohon gwamnan Bayelsa, kuma tsohon ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva (APC), na neman Kotun Koli ta soke nasarar Gwamna Diri.
Za mu ci gaba da kawo maku karin bayani...
Asali: Legit.ng