Bayan Bidiyon Dan Bello, Abba Ya Rasa Goyon Bayan Tsohon na Hannun Daman Kwankwaso

Bayan Bidiyon Dan Bello, Abba Ya Rasa Goyon Bayan Tsohon na Hannun Daman Kwankwaso

  • Yan siyasa a jihar Kano na cigaba da sauya sheka daga jam'iyyun siyasa daban daban tun kafin fara maganar zaben 2027
  • Wasu daga cikin manya a tafiyar jam'iyyar NNPP mai mulkin jihar sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai adawa a Kano
  • Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Barau Jibrin ne ya karbi yan siyasar a ofishinsa da ke Abuja

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya rasa goyon bayan wasu yan siyasa da suka koma APC.

Daga cikin wadanda suka sauya shekar akwai tsohon dan majalisar tarayya Hon. Hamisu Abubakar Lambu.

Barau Jibrin
Tsohon Dan majalisar Wakilai ya fice daga NNPP a Kano. Hoto: Barau I. Jibrin
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanai kan sauya shekar ne a cikin wani sako da Sanata Barau Jibrin ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Rundunar 'yan sandan Kano ta kadu da karuwar asarar rayuka, an gano dalilai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan siyasa da suka sauya sheka a Kano

Tsohon dan majalisar wakilai ta kasa, Hon. Hamisu Abubakar Lambu na cikin waɗanda suka sauya shekar zuwa APC daga NNPP.

Haka zalika shahararren dan siyasa, Muhammad Ladan Kano na cikin waɗanda suka fice daga tafiyar Abba Kabir Yusuf a jihar Kano.

Alakar Hamisu Lambu da Kwankwaso a siyasa

Hamisu Lambu ya zama ɗan majalisar wakilai a shekarun 1993 da 1997 kuma ya kasance mai ba Rabi'u Musa Kwankwaso shawara daga 1999 zuwa 2003.

Haka zalika ya rike mai ba Kwankwaso shawara na musamman daga shekarar 2011 zuwa 2015 kuma ya zama kwamishina a Kano a shekarar 2015.

Shirin APC na kwace Kano a 2027

Yan siyasar sun ce sun koma APC ne domin ganin sun dawo da jihar Kano karkashin APC a zaɓen shekarar 2027 domin kawo cigaba.

Kara karanta wannan

Jihar Kudu ta nemi daukin shugaban APC Ganduje domin ceto siyasar Tinubu a 2027

Sanata Barau Jibrin ya bukaci karin hadin kai tare da cewa APC na kokarin kawo cigaba a Kano a ko da yaushe.

Kano: Yan Kannywood sun sauya sheka

A wani rahoton, kun ji cewa ana kara samun yan jam'iyyar NNPP a jihar Kano na cigaba da sauya sheka zuwa jami'yyar APC mai adawa a jihar.

An ruwaito cewa wasu fitattun jaruman Kannywood sun fice daga tafiyar gwamna Abba Kabir Yusuf suka koma APC ta hannun Sanata Barau Jibrin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng