Kwanaki 7 da Addu’o’in Talakawa, APC Ta Kiɗime, Ta Ba Sanatan da Ya Mutu Muƙami

Kwanaki 7 da Addu’o’in Talakawa, APC Ta Kiɗime, Ta Ba Sanatan da Ya Mutu Muƙami

  • An shiga rundani bayan jami'yyar APC mai mulki ta nada Sanata Ifeanyi Uba cikin waɗanda za su jagoranci yakin neman zabe a jihar Edo
  • Ifeanyi Uba ya rasu ne a ranar 27 ga watan Yuli a ƙasar Birtaniya amma abin mamaki sai ga shi ya fito masu taya APC yakin neman zabe
  • Rahotanni sun nuna cewa wannan ba shi ne karon farko da ake samun mutanen da suka mutu cikin waɗanda aka ba muƙami a Najeriya ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - An hango sunan marigayi Sanata Ifeanyi Uba cikin wadanda APC ta ba muƙamin yakin neman zabe a jihar Edo.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari ana tsakiyar shagalin biki, sun tafka mummunar ɓarna

A watan Satumba mai zuwa ne hukumar zabe ta kasa ta shirya cewa za a gudanar da zaben gwamna a jihar Edo.

Ifeanyi Uba
Sunan Ifeanyi Uba ya shiga cikin masu taya APC yakin neman zabe bayan ya mutu. Hoto: @NGRSenate
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa ko a lokacin mulkin Muhammadu Buhari an ba wadanda suka mutu su shida manyan muƙamai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe Ifeanyi Uba ya mutu?

Legit ta ruwaito cewa Sanata Ifeanyi Uba ya mutu ne tun ranar 27 ga watan Yulin wannanar shekarar.

Sanata Ifeanyi Uba ya rasu ne a Birtaniya duk da cewa ba a gano hakikanin dalilin zuwansa Birtaniyan a wancan lokacin ba kasancewar bai yi wata jinya ba.

APC ta ba Sanata Ifeanyi Uba mukami

Kusan wata daya bayan mutuwa aka hango sunan Sanata Ifeanyi Uba cikin masu taya APC yakin neman zabe da za a yi a Edo.

APC ta nada marigayi Sanata Ifeanyi Uba ne a kan abin da ya shafi harkar kudi domin yakin neman zaben.

Kara karanta wannan

Kisan kiyashi: Yadda maƙabartun Gaza suka cika ana birne gawa kan gawa

Zaben Edo: Sauran wanda APC ta ba muƙami

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio zai jagoranci kwamitin kudi da jam'iyyar APC ta kafa a zaben Edo mai zuwa.

Gwamnan jihar Cross Rivers ne zai jagoranci kwamitin yakin neman zaben gaba daya sai mataimakinsa gwamnan Katsina, Dikko Radda.

Dan takarar APC a Edo ya yi alkawura

A wani rahoton, kun ji cewa na saura mako biyar a gudanar da zabe, dan takarar gwamnan APC ya dauki alkawarin samawa matasa 5,000 ayyukan yi idan ya ci zabe.

A ranar 21 ga Satumba ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta shirya gudanar da zaben jihar Edo, wanda aka dade ana jira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng