INEC Ta Faɗi Gaskiya Kan Sahihancin Sakamakon Zaben Shugaban Ƙasa Na 2023

INEC Ta Faɗi Gaskiya Kan Sahihancin Sakamakon Zaben Shugaban Ƙasa Na 2023

  • Wata ƙungiya ta kalubalanci hukumar zaɓe INEC kan sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 2023 da aka yi
  • Kungiyar CCIJ ta yi zargin cewa akwai saɓanin alkaluma tsakanin sakamakon da INEC ta sanar da wanda jami'ai suka shigar a IREV
  • INEC ta mayar da martani da cewa babu wani banbanci a tsakani, inda ta buƙaci kungiyar ta duba amsoshin tambayoyinta a rahoton zaɓen 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta bayyana cewa babu wani tuntuɓen alkalami ko ruɗani a sakamakon zaben shugaban ƙasa na 2023.

Hukumar INEC ta jaddada cewa sakamakon zaɓen da aka ji daga bakinta bayan kammala kaɗa kuri'u a 2023 sahihi ne kuma ingantacce.

Kara karanta wannan

Shekarau ya bayyana wani babban sirrinsa kafin ya zama gwamnan Kano

Shugaban INEC da Bola Tinubu.
INEC ta musanta ikirarin samun banbanci a sakamakon zaben shugaban ƙasa na 2023 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

INEC ta kuma musanta ikirararin cewa akwai banbancin alƙaluma tsakanin sakamakon da ta wallafa a shafinta na yanar gizo da wanda aka gabatar a ɗakin tattara sakamako.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

CCIJ ta ƙalubalanci sakamakon zaɓen 2023

A wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 7 ga Agusta, wata ƙungiya CCIJ ta yi zargin cewa a sakamakon da aka watsa a talabijin, INEC ta ce ta soke zaɓen akwatuna 1578.

A rahoton Vanguard, kungiyar ta ce jami'an zaɓe sun ce an soke zaɓen akwatunan ne saboda aringizo, tashe-tashen hankula da wasu kura-kurai.

Har ila yau, CCIJ ta ƙara da cewa bayanan da aka shigar a IREV sun nuna cewa jami'an INEC sun sanar da soke zaɓe a rumfuna 2,203 saboda wasu kura-kurai, Punch ta rahoto.

A wasiƙar, ƙungiyar ta nemi karin haske daga shugaban INEC, Mahmud Yakubu, inda ta ce:

Kara karanta wannan

Kotu ta tsige ɗan majalisar PDP, ta faɗi sahihin wanda ya lashe zaɓen a 2023

"Ko za ka mana karin bayani kan yadda aka samu banbanci tsakanin sakamakon da INEC ta sanar da kuma bayanan da ma'aikatan wucin gadi suka shigar?"

INEC ta mayar da martani ga CCIJ

Da yake mayar da martani kan ikirarin ƙungiyar, mai magana da yawun shugaban INEC, Mista Rotimi Oyekanmi, ya ce hukumar ba ta sanar da sakamakon zabe a YouTube.

Oyekanmi ya jaddada cewa babu wani sabanin alƙaluma tsakanin sakamakon da aka bayyana a bainar jama'a da kuma wanda jami'an zabe a akwatuna suka gabatar.

"Kun ambaci bidiyon YouTube guda uku daga gidan Talabijin na Channels, wanda ke nuna yadda aka yi tsakanin baturen zaɓe na Imo, na Abia, da na Zamfara da shugaban INEC a cibiyar tattara sakamako ta kasa, Abuja.
"Abu na biyu muna so ku sani babu wani bambancin alƙaluma na yawan wadanda suka yi rajista ko sakamakon zaben shugaban kasa da INEC ta sanar.

Kara karanta wannan

Jerin muhimman abubuwa 3 da Tinubu ya ƙara masu kudi daga hawa mulki zuwa yau

"Na uku, mun fitar da cikakken rahoton zaɓen 2023 mai shafuka 468 a watan Maris, 2024 kuma mun wallafa shi a shafinmu na yanar gizo, yana tattare da dukkan amsoshin tambayoyinku."

Ayodele ya yi hasashen 2027

A wani rahoton kuma fitaccen malamin kirista, Primate Elijah Babatunde Ayodele ya gargaɗi Bola Tinubu ya tashi tsaye domin daƙile rikicin siyasa.

Malamin ya yi wannan gargaɗin ne a lokacin da yake hasashen abin da zai iya faruwa a zaben shugaban ƙasa mai zuwa a 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262