"Ku Yi Hankali da Yan Siyasa": Sanata Ya Yi Martani ga Masarauta Bayan Rasa Rawani
- Sanatan Bauchi ta Kudu, Shehu Buba ya yi martani kan tube shi da aka yi daga sarautar Mujaddadi bayan sukar gwamna
- Sanata Buba ya ce ya karbi wannan hukunci hannu bibbiyu inda ya roki Allah ya kawo mai ceton jihar daga wannan kangi
- Hakan na zuwa ne bayan tsige shi daga sarauta da masarautar Bauchi ta yi kan sukar Gwamna Bala Mohammed kwanan nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Bauchi - Sanata Shehu Buba ya mayar da martani bayan tube shi a sarauta da aka yi a jihar Bauchi.
Sanatan ya shawarci masarautar Bauchi da ka da ta bari a yi amfani da ita wurin zurma ta a cikin siyasa.
Sanata Buba ya kaɗu da hukuncin masarauta
Wannan na kunshe ne a cikin wata wasika da ya fitar inda ya ce ya yi wa gwamnan ne martani da kyakkyawar niyya, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanatan ya nuna damuwa kan yadda masarautar ta dauki zafi tare da yanke hukunci ba tare da tuntubarsa ba.
"Na yi magana da kyakkyawar niyya kuma da kare wanda ya fi gwamna matsayi ne, abin takaici ne yadda masarautar Bauchi ta yanke hukunci ba tare da jin ta bangare na ba."
- Sanata Shehu Buba
Bauchi: Sanata Buba ya karbi ƙaddara
"Na karbi wanna hukunci da hannu bibbiyu kuma ina rokon Allah ya kawo wanda zai tsamewa Bauchi kitse a wuta."
"Ina shawartar masarautar Bauchi ta yi hankali da yan siyasa wurin yin amfani da ita domin cimma burukansu, ina yi wa Sarkin Bauchi fatan alheri da karin lafiya."
- Sanata Shehu Buba
Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Bala ya caccaki Bola Tinubu kan halin kunci da al'ummar Najeriya ke ciki.
Masarautar Bauchi ta tube sanata daga sarauta
Kun ji cewa masarautar Bauchi ta tube Sanata Shehu Buba daga sarautar Mujaddadin Bauchi saboda sukar Gwamna Bala Mohammed.
Sanatan da ke wakiltar Bauchi ta Kudu ya caccaki gwamnan ne bayan shi ma ya soki Shugaba Bola Tinubu kan tsare-tsarensa a Najeriya.
Majalisar masarautar ta tabbatar da janye sarauta daga kan sanatan a wata wasiƙa mai ɗauke da sa hannu madadin sakataren fada.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng